Tsaro: 'Yan Ta'adda Sun Yankawa Manoman Zamfara Harajin Girbi

Tsaro: 'Yan Ta'adda Sun Yankawa Manoman Zamfara Harajin Girbi

Al’ummomin karkara da ke cikin Karamar Hukumar Bungudu a Jihar Zamfara sun sake tashi da wata sabuwar matsala saboda ƴan ta'adda. Rahotanni sun iske jama'a na cewa nuna ’yan bindiga sun ƙara matsa lamba tare da kakaba haraji mai nauyi kan manoma da ke son girbe amfanin bana. 
Mai sharhi a kan harkokin tsaro a yankin Arewa maso Yamma, Bakatsine, ne ya wallafa hakan a shafinsa na X a ranar Juma’a. 
Rahoton ya ce wadanda abin ya shafa sun ce a yanzu ba a bari manoma su kusanci gonakinsu sai sun biya kudin da ’yan bindigan suka ce dole sai an biya. 
Al’ummomin Durkai, Honkarhe, Makwa da Kiluta ne suka fi fuskantar wannan matsin lamba, inda ake zargin cewa sun ɗorawa kowane yanki kuɗin da ya zarta ƙarfin jama’ar da ke zaune a can. Wani mazaunin yankin ya shaida cewa,: "Manoma a Durkai, Honkarhe, Makwa da Kiluta since an ɗora masu harajin girbi mai nauyi kafin su ciro amfanin gonakinsu." 
Ƴan ta'adda sun dora wa kowane manomi a Durkai da Honkarhe harajin girbi da ya kai N5m.
Wadannan buƙatu sun saka jama’ar yankunan cikin fargaba da tashin hankali, musamman ganin cewa manoma su ne ginshiƙan tattalin arzikin yankin. Rahotannin sun ƙara bayyana cewa lamarin ya kai wani mataki mai ban tsoro, inda ake zargin ’yan bindigan sun fara sa farashin kayayyaki, musamman babura. Mutane a yankin sun ce farashin babur ɗin Honda ya kai kusan N1.7m saboda tsoma bakin ’yan ta’addan a kasuwa.