MAMAYA: Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita Ta 23

Page __23
Sai da Baba ya gama komi a kasuwar sannan ya sayi ɗan balango mai romo-romo ya nufi gida da tunanin yanzu dai Nasir ya maida Bilkisun gida, sai ta samu ta ɗan ci naman da zafinsa, ya sake siyen lemu mai sanyi ya haɗa ya nufi gidan.
Yana sauka a keke napep yaga gidan a kulle, abin ya bashi mamaki, musamman da yasan cewar yayima Huraira kashedin fitar da take idan ya fita, makwabtansu ya aika ko tana can amma akace bata can, yanzu yasan cewa Nasir bai maido Bilkisun ba, dan da ya maidota Huraira bata rufe ta cikin gidan ta tafi yawonta.
Yana cikin tunanin wani matashi yayi masa sallama, suka gaisa cikin ladabi ya shaida masa ƙanin Nasir ne, ya bashi makullin gidan yace kuma Bilkisu gado aka bata asibitin Inna Huraira nacan tare da ita. Gaba ɗaya sai hankalinsa ya tashi, kar dai ace dukan ya jawo wata matsala gareta ? Ajiyar zuciya yayi yace "Yaro ba sai na shiga cikiba kawai muje ka kaini asibitin Allah ya kyauta" tare suka nufi asibitin sojoji dake hanyar Kaduna , banda addu'a babu abin da Babansu Bilkisun keyi, iyakar damuwa ya damu amma sai ya boye dan baisan Nasir ya fahimta harma yaji ƙwarin guiwar aikata wani lamarin, a haka suka isa har zuwa ɗakin da Bilkisu take kwance. Sun iske ana fama da Inna Huraira ta tsaya ai mata allura wai itama bata lafiyar amma ta dage sai zagin likitar take,abin sai yaba Malam haushi, ya daka mata tsawa yace "Wai ke Huraira yaushe zaki yi hankali ne ? Yara sun fiki natsuwa da sanin ya kamata, duk ranar duniya sai kin abin da kika ɓatamun rai, to ki natsu ai maki kafin yanzun nan na baki mamaki. Kallonsa tayi da niyyar caɓa masa magana sai taga yayi mata kwarjini ba zata iya gaya masa abin da ke bakinta ba, dan haka ta juya likitar ta danna mata sirinjin (injection)ai kuwa ta kwarma uban ihu tana tsinema likitar ta uwa ta uba. Bilkisu banda hawayen takaici babu abin da take jin daɗin ta guda Ibnah nanta ya fita,tabbas da Inna ta gama bata kunya iyakar kunya agunsa, yanda ta dinga ihu tana zagin likitar tana tsine mata kamar wata ƙaramar yarinya. Likitar ta dubi Inna Huraira tana mulmushi tace "Tsohuwa ba juriya ki natsu karki taɓa ruwa duk yau kinji ? Kallon sannu uwata Huraira tai mata kafin tace "Tunda ke kika haifeni ai kin ban doka shegiya irin mugayen Aljanu kawai, yanzu zan fara amfani da ruwa ki dawo ki mun wata inkin cika tabbatatta" shi dai Malam kai tsaye gun Bilkisun ya nufa yana ƙare mata kallo duk ta faɗa ga shedar duka ko ina a jikinta gefen idonta ya kumbura, da ganinta kasan tana jin ciwo, girgiza kansa yayi yana jin tausan yarinyar sam barayi dacen uwaba , ya dubeta da tausayawa yana mata sannu, ya fito da naman da lemun ya tadata zaune yana umartarta da taci, "Baba kaba Inna taci sannan" ya dubeta kamar yayi hawaye yace "Naki ne wannan Bilkisu idankika gama sai kibata sauran ........bai ida maganar ba Inna Huraira ta wafce naman har yana zubewa ƙasa "Wallahi Malam baka isaba, shine tsabar son kai zaka siyo naman ka tasa matashi gabanta ita kaɗai? To ba zan lamunta ba" taci gaba da watsa tsokar naman bakinta tana mitar sauranma idan ta ragye ƙananan yaranta zata kaima tsaraba, ba zata bata shiba, wanda ke kwance gadon asibiti ana ɗura masa ruwa ta wani nama yake indai da gaske ciwon na Allah da Annabi ne ? Malam ya yunƙura kenan zai tashi Major Nasir ya shigo tare da wasu sojoji riƙe da manyan ledoji shi kuma Major Nasir yana ɗauke da kular abinci , ai nan take Inna Huraira tayi wuri-wuri da idanunta , tsoro ya bayyana ga fuskarta ta kasa haɗe naman daje bakinta , wanda hakan yasa ta ƙware da gudu ta nufi toilet tana ƙoƙarin amai, tana shiga taga ruwa cikin wata roba bata jira komi ba ta fara sha tana wanke fuskarta, har sai da taji tarin ya lafa mata sannan ta fito tana jin wani zafi cikin kwanyar kanta.
Cike da mutuntawa suka gaisa, Malam na tambayar Nasir mai jiki , yana da sauƙi . Ya dubeta cikin kulawa yace "Ibnah-Nas nasan baki ci komi ba maza tashi kici abinci " tuni sauran sojojin sun fice daga shi sai Malam da Inna Huraira dake soshe-soshe kamar sabuwar kamu, kallonsa tayi najin kunyar sunan daya ambaceta dashi gaban Babanta take, shi kuma sai ƙoƙarin buɗe kular yake, wani ƙamshi ya mamaye ɗakin baki ɗaya, ya miƙa mata kulan gabanta yana cewa "Ibnah-Nas maza ki cinye wannan sai ki ƙara da wani abun kinji ? Kular ta kalla sai da miyanta ya tsinke ganin lafiyeyyen farfesun kayan ciki sunsha gyara sai ƙamshi suke, ya aje mata goron ruwa da lemun kwakwa yana ta mulmushi kamar yanda shima Malam keta murmusawa.
Ta natsu ta fara cin naman kenan Inna Huraira ta fasa uban ihu ta fara mirgina ƙasa tana cewa "Allah ya isa duk wanda ya samun karara wallahi ba zan yafe masa ba duniya da lahira" taci gaba da soshe-soshe tana ta bani Malam ka sosa mani, dan Allah ka sosa mani , wayyo malam ka sosa mani .
Gaba ɗaya kunya ta gama kama Malam musamman yanda ta saki zanenta ta fige kallabinta wani mahaukacin gashi duk ƙuda-ƙuda ya bayyana tana birgima tana gantsarewa wai ya sosa mata. Major kam kallo guda yayi mata ya kauda kai yaci gaba da kallon Bilkisu dake neman fashewa da kuka, kallon karki mun kuka yayi mata, ya dubeta yana murmushi yace "Ibnah-Nas bari naje na duba wani awaje amma ki tabbatar baki rage komi ba cikin kular nan ba kinji ? Kai kawai ta ɗaga masa dan tana magana kuka zai fito, batasan abin da yasa Inna ke mata hakaba, duk sanda Ibnah yazo saita bata kunya amma ta yau tafi muni .
Kasa tankama Baban yayi dan yaga yanda ranshi ke a jagule ya nufi kofar fita, kawai ji yayi Huraira ta riƙe masa kafa tana cewa "Taimaka ka sosamun,dan Allah ka sosamun, wayyo zoka sosamun" Baba da takaici ya ida kashewa ya taso ya kwace masa ƙafarsa yace "Inka fita ka turomin likitar mahaukata Nasir Allah ma albarka. Shi dai yana jin ya sakar masa kafa ai sai yayi wuf ya fice yana jin garama da iyayensa basu biyoshi ba da yau matar nan ta zubar masa da komi yasan ko Abbansu bai magana sai Ummarsa tayi kuma ƙannensa da sun rainasa.
Yana fita Malam ya tadata zaune yace kin kyauta kin zubar Mani da mutunci Huraira yanda ya kamata muje gida nasan Nasir ya tafi kenan bai dawowa, ya dubi Bilkisun dake kuka sosai yace daure mutafi gida yarinyar kirki ta ɓata komi. Wani irin faɗuwar gaba ta sameta jin furucin Baban, itakam yau ba sai gobe ba zata so jin wa ce ce mahaifiyarta ta gaske daga gun mahaifin nata, abubuwa da dama sun bayyana ba Innar tasu ce ta haifeta ba .
Itakam Huraira da gaske take jikinta baki ɗaya kaikai yake mata na bala'i amma Malam ya kasa sosa mata ai kuwa yau zakaga haukan karya, musamman dataji yace shegen yaron can Nasir bai sake zuwa gunsu. Ta miƙe tsaye da ƙyal tana soshe-soshe tayi waje haka Bilkisu da Malam suka rufa mata baya suma.
Suna fitowa suka samu wani soja da akace ya maida Malam ya kwashesu ya nufi gida, Inna Huraira sai mutsu-mutsu take cikin motar har suka isa gidansu.
Yana tsaye riƙe da ganyen karara suka zo suka wuce shi zuwa cikin gidan Inna Huraira na zuwa ya watsa mata shi ya ɓace yana gaggaɓa dariyar mugunta .
To fa ya kenan jama'a ana kukan targade sai ga karatu ga Inna Huraira ?
*Taku ce Haupha