Gwamnatin Zamfara Ta Haramta Hawa Babura, Ta Ce Duk Wanda Aka Gani a Sama  a Harbe

Gwamnatin Zamfara Ta Haramta Hawa Babura, Ta Ce Duk Wanda Aka Gani a Sama  a Harbe

 
Duba da sake tabarbarewar tsaro a Zamfara, Gwamna Bello Mattawale a ranar Litinin ya haramta hawan babura daga karfe 8 na dare zuwa 6 na safe a garin Gusau.
Ya umurci jami’an tsaro da su harbe duk wanda aka samu ya saba wannan sabon dokar, kamar yadda Punch ta ruwaito.
A cewar gwamnan, an dauki matakin ne biyo bayan rahotannin yadda ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka ke amfani da babura wajen aikata muggan laifuka a cikin babban birnin jihar da kewayenta. 
“Wadannan yankuna sun hada da Mareri, Damba, Tsunami, Tsauni, Barakallahu, Samaru, Gada Biyu, da Janyau Gabas”.
“An umurci jami’an tsaro da su bindige duk wanda ya hau babur tsakanin karfe 8 na dare zuwa karfe 6 na safe a wajen garin Gusau, wanda ya ki tsayawa idan aka umarce shi da ya yi hakan.
“A halin da ake ciki, an yi kira ga jama’a da su sanya ido a yankunansu tare da kai rahoto ga jami’an tsaro na duk wani mutum da ake zargi ko wani bakon motsi a yankunan.” 
"Gwamnatin jihar ba za ta yi wasa da duk wanda aka samu yana kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron jama'a ba". Gwamnan ya jaddada cewa, tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa shi ne babban aikin kowace gwamnati, kamar yadda SolaceBase ta kawo.