MAMAYA:Labarin Soyayyar Mutum Da Aljani, Fita Ta 31 Zuwa 32
Page 31____32
Cike da mamaki Nasir ke kallon magen,sai wani ƙara zare masa idanuwa take suna wani ƙara haske tamkar an haska fitila, taɓe bakinsa yayi ya runtse idonsa dan yana son sake jin muryar Ibnarsa a cikin kunnuwansa yanda take amayar da abin da ta jima tana dako a ƙasan zuciyarta ya tafi da imaninsa baki ɗaya. Sai dai madadin ya dinga jiyo sautin muryarta da hasasota cikin idanunsa,sai ma ya dinga jin gurnanin mage da ganinta tana komawa kala daban-daban, a cikin idanunsa,hakan yasa shi jan tsaki ya buɗe idonsa ransa har ya fara ɓaci, ba inda idanunsa suka sauka sai kan magen nan, wannan karon ta sauya kama ta koma irin mai gashin nan tamkar kura,idanunta babu haske ko kaɗan sai cin wani ɗanyen nama take jini na ɗiga daga cikin naman. Zuwa yanzu jikinsa ya gama bashi cewar magen ɗazun ce ta gayyato masa mazuru harma da naman sata dan iskanci su rasa inda zasu ci naman sai ɗakinsa, duk dan suyi masa ƙazanta ko ? To duka zai haɗesu yayi maganinsu a yau,yanzu bama sai gobe ba, wayarsa ya ɗauka ya kira yaransa Samu yace masa"Maza ka kama magen can ka fitar waje ka halbe su duka har ta wajen ma. Samu ya duba tas amma baiga komi ba dan haka ya dubesa cike da gamsarwa yace "Sir ba wani mage a nan na duba. Inda magen take ya kalla ai kuwa ya zubama Samu ido yana mamakin abin da ya samesa da baiga magunan har biyu ba da suke ta cin ɗanyen nama ba,har wani gurnani suke tamkar zakuna dan samun waje.
Cikin tsawa yace ma Samu "Kana nufin baka gansu ba har yanzu ko kuwa ? Cike da bin umarni Samu ke dubawa amma baiga komi ba,hakan yasa ya fita ya kira abokin aikinsa Nura su duba tare,zuwa lokacin Nasir ya gama ƙulewa da magunan yanda suke ta yaryaɗa masa jinin naman a tsakar ɗaki. Shigowarsu Samu ne yasa ya fasa nufinsa kan ƴan iskan magunan,so yayi ya miƙe ya rufe ɗakin yaci ubansu da kansa kana ya bada su a kashe su a yarda gawar koma na uban wa ne ne a cikin barikin. Abin mamaki wai har Nuran ma bai gansu ba, bacin gasu yana gani sunata muzurai da iskancin cin naman, hanya ya gwada masu kawai yace "Kuje bakin aikinku kawai "suka fice suna tunanin ko dai shima ya fara kwalfewa ne irin na wasu daga cikin su? Basu da amsar dan haka suka bakinsu sukai shiru da maganar.
A can cikin ɗakin kuma,su Nura na fita magunan suka fara gaba faɗa da junansu tamkar zasu kashe kansu, hakan yasa ya gyara kwanciyarsa yana kallon yanda suke faɗan tamkar wasu mutane ko manyan namun daji,kallonsu yake yana son fahimtar wani abu a cikin faɗan nasu, idan ya fahimta dai-dai magen farkon nan ce ke son ta tare mai gashin yana son ya iso gunsa ita kuma tana hanawa, wasa-wasa sai gashi wancan yaji mata wani rauni mai girma har sai da tayi wani irin nishi gwanin tausayi,kawai tsintar kansa yayi da miƙewa tsaye bakinsa na furta "A'uzubillahi minasshaiɗanirrajim". Kai tsaye ya sunkuya ya wawuri mazurun ya dinga bugashi ga bango sai da yaga jini na zuba kana ya wurgashi ta taga. Tsaki ya ja ya sunkuci gudar magen dake baje tana maida numfashi ya tsira mata ido yana jin tausanta a ƙasan zuciyarsa, itama magen sai tayi luf tana kallonsa tamkar masu magana da idanuwansu, da sauri ya aje ta kan kujera ya fice da zummar samo mata magani.
Yana fita magen tayi girgiza ta koma kyakkyawar mace, gefen kanta da rauni jini na ɗiga marar kyan gani, cike da gamsuwa ta bushe da dariya tace "Na rantse da wanda ya busamin numfashi a ruhina ba zan taɓa bari ka nakasa masoyina ba Yah Malam, taƙamarka izza gadara da sarauta to wallahi nafika nasaba da karfin siddabaru kafi kowa sanin mahaifina Zayyanul murrash bin zainul shine Sarkin bokayen duk wani tantiri ko takaɗari, na bar komi nawa ne saboda ina son Nasir duk da kasancewarsa bil'adama,to akansa na musulunta haka akansa zan koma gadona dan kawai nai gadinsa. Ta sake girgiza ta koma magen ta langaɓe kamar mai barci .
"Gaba ɗaya Huraira kin matsa mana da turarki a cikin gidan nan, to yau dai zamuyi ta a faifai mu da ke saboda mun lura kinyi degree a fannin masifar tsiya ko ? Huraira da tunda ta faɗa ɗakinta ta rufe ta fara tsinar duk aljanin da ke takura mata, a tunaninta ta tsira domin ta amso wata laya gun wata ƴar bori ta tabbatar mata cewar babu aljanin da zai sake shigar mata ɗaki indai layar na cikinsa. Hakan yasa tana ganinsa ta faɗo ɗakin ta kama tsine masu albarka, sai dai jin wancan furucin yasata ɗagowa dan ganin wake maganar? Wata mata ce ita ba sama ba ita ba ƙasa ba, hannunta akwai wata sharɓeɓiyar bulala mai baki biyu, idan ba ƙarya idonta ke mata ba muguwar malamar likitar nan ce wadda ta ɗagata sama dan zalunci sai da ta jiyo ƙamshin mutuwa kana saboda rashin tausayi ta sakota ƙasa tim kamar kayan wankin da cuta. Cike da ƙwarin gwiwa Huraira ke duban Aljanar dan mai maganin ta tabbatar mata da cewar ko sun shigo ɗakin to basu isa su cutar da ita ba,sai dai ita ce ma zata iya cutar dasu, tuni hakan yasata a nishaɗi harma ta samu damar gyara tsayuwarta ta kalli Aljanar ta kwashe da dariya kamar irin basawan nan, ita a dole zata ɗauki fansar abin da tai mata a asibiti ,sai da tayi mai isarta kana ta haɗe ranta,ta kalli madubi taga tabon marin da tai mata, ta ɗauki kwallin magani shima ta shafa duk abin da take Aljanar na yanda take tana kallonta bata ce mata ƙalla ba tana jiran taga abin da zatai mata ne .
Huraira ta dubeta fuska ba annuri tace "Sauko ƙasa dan ubanki ! Yau zaki ga tujara iya tujara, masifa iya masifa, dan yau sai na saka kin tunani Kakan ubanki na ƙarshe dan bala'i na." Sai kuwa Aljanar ta sauko ƙasa kanta sadde Huraira ta fisge bulalar ta shauɗa mata tana ƙara kallon inda ta aje layarta .
Tunda ya kaita gidansu yake jin ba daɗi, gaba ɗaya fuskarta ta tsaya masa a zuciya, so yake ya sake ganinta ko da ba zai ce mata komi ba,(Malam Aminu kenan) hatta abincinsa ya kasa ci, ita kawai yake son sanin halin da take ciki yanzu, yawo yake tsakar ɗakinsa yana kaiwa da komowa, haƙiƙa Bilkisu abar tausayi ce a garesa,haka kawai yake jinsa tamkar wani wanda ya rasa wani jigo a tare dashi, ƙarshe alwalla yayi ya kama sallah yana roƙa mata sauƙi ga ubangiji, yayi mata addu'a sosai sannan ya sallame ya kwanta yana jin tamkar shima bai da lafiyar.
Shema'u bata tsaya ko ina ba daga islamiyar kai tsaye gidansu Bilkisun ta nufa dan ganin halin da take ciki yanzu, ita kam da Bilkisu zata burgeta data rabata da Nasir dan wallahi tsoronsa take sosai ba kamar yadda ya dinga kabtar Malam Aminu ba tausayi duk da yana namiji ina ga ita mace ? Ya shaida mata duk abin da faru da Bilkisu ta tabbatar ta kira ta faɗi idan ba haka ba zai ɓata mata rai, soja ya ɓata ma mutum rai dai-dai yake da shiga tawaye rayuwa kuwa, da wannan tunanin ta isa gidansu Bilkisun,sai dai ta iske ta sai barci take abinta sai dai zafi da jikinta ya ɗauka alamar har yanzu akwai zazzaɓi tare da ita .
Ko mi zai faru da Inna Huraira da ta fara ramuwar gayya ga Aljana ?
Shin wa ce ce Aljanar da ta kare Nasir daga harin Yah Malam ?
Miye gaskiyar abin da ke zuciyar Malam Aminu gane da Bilkisu ?
Duk Haupha ke da amsarku dan haka ku jirata a page nagaba
managarciya