Gwamnonin PDP Sun Rabu Gida Biyu kan Batun Sauke Shugaban Jam'iyya Na Ƙasa

Gwamnonin PDP Sun Rabu Gida Biyu kan Batun Sauke Shugaban Jam'iyya Na Ƙasa

 
Ga dukkan alamu rikici ya ɓarke a tsakanin gwamnonin PDP kan batun muƙaddashin shugaban jam'iyyar na ƙasa, Umar Damagum. 
Ana ganin dai wannan babban matsala ce ga PDP a daidai lokacin da take ƙoƙarin warware duk wata rigima a cikin gida musamman rikicin Ribas. 
Jaridar Punch ta ruwaito cewa kiraye-kirayen a sauke shugaban PDP Umar Damagum, ya raba kawunan mambobin ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar. 
Shugaban gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya ce sun fara aiki da kwamitin gudanarwa NWC domin karɓe kujerar Damagum. 
A ɗaya ɓangaren kuma Gwamna Seyi Makinde ya ce ba ya goyon bayan canza Umar Damagum daga shugabancin PDP. Wani babba a kwamitin NWC na PDP ta ƙasa, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce bayan Nyesom Wike, Damagum ya ƙara samun goyon bayan gwamnoni huɗu waton Gwamnonin Adamawa da Taraba da Filato da kuma Osun.