WATA UNGUWA: Fita Ta 12
Sannu a hankali ƙananan matsalolin nan suka fara rikiɗa suka zama manya har ya haifar da saki a tsakaninsu. Da ta koma gida Abbanta ya hana mata zama, ga shi ta kasa kusantar ƙofar gidan yaya Aminu da sunan zama tunda ta sani sarai Habibu ƙaninsa ne ɗan wa da ƙani suke kuma suna matuƙar ji da junansu. Ina! Ai ko da wasa ma ba zata iya gwada aikata hakan ba, abun da kunya. Dalili kenan da yasa ta jure zama a gidansu duk da horon da Abbanta ya yi mata ta hanyar jibga mata duka aikin gidan gaba ɗaya.
BABI NA SHA BIYU
"Zubairu me kake shirin aikatawa ne?" Ta faɗa muryarta na rawa.
Saurin sauke yarinyar ya yi daga cinyarsa ya miƙe yana 'yan kame-kame.
"Me kika gani ne? Kuka fa na tarar tana yi shi ne nake rarrashinta" ya faɗa.
"Ka dai ji tsoron Allah, ka sani duk abun da kake aikatawa Allah na ganinka domin Ubangiji baya barci balle gyangyaɗi." Ta faɗa yayin da take binsa da kallon tuhuma.
Ɗaga kafaɗarsa ya yi irin ko ajikinsa ɗin nan ya zo zai wuce ta yana Faɗar "Dama wani kyakkyawan albishir na zo gaya miki amma kin ɓata rawarki da tsalle, tunda ki ke zargina, ni na yi gaba."
Har ta buɗe baki da nufin ta dakatar da shi, sai dai kafin ta kai ga motsa harshenta ya fice daga gidan.
Tana ganin haka kawai sai ta ƙarasa cikin ɗakin inda ta tarar da Salma tana sauke ajiyar zuciya alamar ta sha kuka, fuskar nan duk ta yi jirwayen hawaye.
Kallon Salma ta yi ta ce "Ke kuma menene? Kin san Allah Salma idan baki daina koke-koken munafurcin nan da kika tsira kwanan nan ba ni da ke ne. Wannan da 'yar kishiya ce ke ai sai ki saka a zargi ko ina zaluntarki ne."
Shiru yarinyar ta yi bata ce komai ba, sai ci gaba da sauke ajiyar zuciya da take.
Fizgo hannun yarinyar ta yi da ɗan ƙarfi "Ni don Allah taso na miki wanka duk da dai shekaranjiya na miki wanka, amma ko don tsoron masifar fitinannen mahaifinki dole na kuma miki wani yanzu."
Tsakar gidan ta fita da ita ta mata wanka tana tsaka da shirya yarinyar ne ta tuno da bikin ƙanwar ƙawarta da ta gayyaceta ga shi kuwa ta manta bata sanar da Habibu ba, amma ta kudurce a ranta sai ta je, in ya so in ya dawo gida sai ta gaya masa ta fita.
Cikin gaggawa ta ci gaba da gudanar da aikinta, yau kam sai da ta share ko ina tsaf, ta yi lafiyayyen girki ta saka a kula ta ajiye masa a falo, wai ko da zai dawo ya tarar bata nan.
Ɗibar abincin ta yi ita ma ta ci sannan ta sanyawa Salma nata tana ci, a uzurce ta shige banɗaki ta yo wanka mai kyau, wanda marabin ta da yin kyakkyawan wanka tun bikin Basira da yake shi ne biki na ƙarshe da ta fita sai kuma yau da ta ke shirin fita. Sauran ranakun da take gida kam ko ta yi wankan asarar sabulu da ruwa ne kawai, don jiƙa datti kawai take.
Bayan ta fito ta buɗe lokar kayanta, ta zaɓo na can ƙasa.
Wani lace ne dark purple mai masifar kyau, da ganinsa kasan zai yi tsada ko da ba sosai ba.
Zaunawa ta yi ta tsantsara kwalliya irin wacce take yi Lokacin tana budurwa, ta saka lace ɗin nan sannan ta kashe ɗauri.
Abu ga farar fata sai ta fito cas abunta kamar ka sace ta ka gudu.
Wanda bai mata farin sani ba idan ya ganta a ranar zai iya rantse cewa ba Biba ƙazamar da ya sani ba ce.
Mayafinta ta yafa sannan ta saka turare sama-sama, ta fito tare da kulle ƙofar ɗakin.
Hannun Salma ta ja suka wuce bayan ta kulle gidan da maƙulli.
Salma ta kalle ta cikin alamar mamaki ta ce "Mama ina zamu? na ga yau kin yi kwalliya."
Murmushi ta jefi yarinyar da shi ta ce gurin biki za ni Salma.
Da walwala a fuskar yarinyar ta ce "Kin yi kyau Mama, kin wanku fa."
Daɗi ta ji sosai a ranta, sai murmushi ta ke zabgawa.
Salma na ganin sun shiga layin gidan yaya Hanne ta ce "Mama ba kin ce biki zamu ba?"
"Biki dai za ni Salma, zan kai ki gun yaya Hanne ki jira ni, zan taho miki da kayan biki kin ji?." Ta faɗa da sigar rarrashi.
Yarinyar ta so ta saka rigima, sai dai ta san wannan ba mafita ba ce, domin a maimakon Maman ta ji tausayinta ta tafi da ita, zama ta iya dukanta. Hakan yasa ta yi shiru har suka isa gidan Yayar.
"A'ah! Ƙanwata an sha ado sai ina haka?" Yaya Hanne ta faɗa da mamaki a fuskarta.
Dariyar jin daɗi Biba ta yi ta ce "kai Yayata! Banda zolaya fa. Wallahi bikin ƙanwar Hadiza ƙawata za ni a unguwar Dagarma.
A nan yayar ta mata fatan dawowa Lafiya sa'annan ta fice daga gidan.
Tun kafin ta ƙarasa titi magulmatan unguwa ke binta da kallo suna zunɗenta a zuciya har ta zo titi.
Tana tsaye tana jiran Napep sai ga Mamuda s/m ya zo wucewa. Duk da cewa duk waɗanda suka ganta sun yi mamaki kuma sun yi gulmarta a ransu, amma ba wanda ya tamka sai Mamuda, ko da yake shi ba ya gani ya ƙyale.
Yana zuwa dai-dai ita ya washe haƙora "A'ah! Wa nake gani haka kamar Bibalo?" Ɗan murmushi ta yi ta ce "eh ni ce ina wuni?"
"Lafiya qlau, za'a fita kenan? To Allah ya sa dai da sanen gola za a jefa ƙwallo raga."
Duk da cewa watarana Bibar Sakara ce, amma fa yau sarai ta gane me yake nufi don haka ta yi ɗan guntun murmushi ta ce "Ah! wannan ai ba abun damuwa ba ne, ka kula da akuyoyin da ke gabanka na lura da sun fara ƙosawa....." Iya haka ta gaya masa tare da tare Napep ta shige abunta nan ta bar shi tsaye yana ta tunani 'to ina kalamanta suka dosa?' can kuma sai ya tuna da yana da ƴaƴa mata ba mamaki su take zagi a fakaice. Sosai ya ji ciwo a ransa sai dai baya da wani abu da zai iya aiwatarwa akan hakan.
Ita kuwa Biba tana cikin Napep sai zance take ita kaɗai "Munafukin banza da wofi, wato yana nufin Allah ya sa da sanen Mijina na fito, ko da yake bai kamata na damu ba tunda na mayar da dai-dai abun da aka gaya mun."
Mai Napep ɗin ya na jin ta sai dai bai ce komai ba girgiza kai kawai ya yi yana mamakin halin wasu matan, 'lallai wannan zamani abin tsoro ne ya faɗa a ransa.'
WACECE BIBA?
ASALINTA
Habiba 'ya ce ga Alhaji Sule Ya'u mazaunin unguwar Saminaka a jihar ta MAMBIYA, yana da rufin asirinsa daidai gwargwado, matansa biyu Jimmala da Zaliha. ƴaƴansa goma.
Jimmala ita ce uwar gida tana da yaya biyar, Hannatu ce babbar 'yarta sai Habiba sannan Zainab, sai Haidar sannan Auta Sa'adiya. Yayında Zaliha ita ma take da yaya biyar, Uku maza biyu mata.
Rayuwar gidansa abun burgewa ce akwai haɗin kai sosai a tsakanin matan matsalar ɗaya ce Zaliha ƙazama ce ta ƙarshe ita ma ɗakinta ba ya shiguwa saboda shirgi da tarkace, Jimmala ita ce ke jajircewa da iya ƙarfinta da na yaranta su gyara gidan.
Bayan Hanne ta yi aure sai nauyin ya dawo kan Inna Jimmala da 'yarta Zainab domin dama can Biba bata son karya jikinta ko kaɗan tun Innar tata na sababi kamar zata aro baki, har ta gaji ta daina.
Bayan auren Hanne da shekara ɗaya ta haihu ta zo gida zaman jego, lokacin da zata koma ne aka bata ƙanwarta Biba da a lokacin ta ke da shekaru 13 don ta taya ta reno. Tun daga lokacin riƙon Biba ya koma hannun Hanne da mijinta Aminu su ne komai nata. Baba ya so ta dawo gida kamar me, sai dai ba zai iya watsa ƙasa a idon surukinsa da yake matuƙar ganin darajarsa ba. Ba yanda za'ayi ya iya saka hannu ya ture ƙoƙon barar da sirikin nasa ya miƙo masa, hakan ya saka akan tilas ya yarda ya ba shi Biba ta koma zama gurinsu a unguwar Garwa har zuwa lokacin da ta yi aure.
Aurenta da Habibu aure ne na soyayya da ƙaunar juna, lokacin da take kan ganiyar ƙuruciyarta 'yar gayu ce ta ƙarshe, ƙwararriya ce a gurin iya tsara ado, da yake Aminu yana kula da ita sosai kamar ƙanwarsa ta jini.
Tun lokacin da Habibu ya ƙyalla ido ya ga Biba a unguwarsu kuma a gidan ɗan uwansa, tun lokacin ƙaunarta ta ɗarsu a ransa sannan ya ɗaurawa gidan Yaya Aminu aure.
Tun yana ɓoyewa har ya kasa jurewa ya samu yaya Hanne da zancen ta yi murna sosai da hakan, domin ta yaba da hankalin Habibu kuma ta san ko su waye iyayensa don haka ta shaidawa mijinta shi ma ya yi farinciki da hakan. Hankalinsa zai fi kwanciya idan amanarsa ta kasance a hannun ɗan'uwansa da yake matuƙar ƙauna. Sai dai da yake lokacin suna yi mata kallon ƙaramar yarinya hakan ya saka suka ba shi shawarar ya bari ta ƙara girma zuwa lokacin shi ma ya kimtsa.
Hakan ya saka ya yi shiru har bayan wasu shekaru. Lokacin da maganar ta yi ƙwari suka kaita gaban iyaye, kasancewar yaran sun haɗa kansu. Cike da farinciki aka ɗaura auranta da Habibu a ranar wata Asabar, ranar ta yi daidai da ranar da ta cika shekaru goma sha tara a rayuwa.
Bayan auren amarya ta tare a gidanta da ke bayan layin gidan yaya Hannen.
Soyayya suke Shimfiɗawa cike da kwanciyar hankali, kullum gidan a tsaftace gwanin burgewa.
Bayan watanni goma da auren Biba ta santalo 'yarta kyakkyawa wacce ta so ma ta fi ta kyau, ranar suna yarinyar ta ci sunan Salma.
A gidan yaya Hannen ta yi zaman jego bayan wasu watanni ta koma ɗakinta. To daga lokacin ne ƙananan matsaloli da rigingimu suka fara ɓullowa a gidan. Hakan ta faru ne silar wasu halaye da Biba ta tsiro da su wanda da bata da su, halayen kuma su ne ƙazanta ƙananan maganganu da tsegumi, a lokacin ne kuma ta fara tara matasa a gidan.
Sannu a hankali ƙananan matsalolin nan suka fara rikiɗa suka zama manya har ya haifar da saki a tsakaninsu. Da ta koma gida Abbanta ya hana mata zama, ga shi ta kasa kusantar ƙofar gidan yaya Aminu da sunan zama tunda ta sani sarai Habibu ƙaninsa ne ɗan wa da ƙani suke kuma suna matuƙar ji da junansu. Ina! Ai ko da wasa ma ba zata iya gwada aikata hakan ba, abun da kunya. Dalili kenan da yasa ta jure zama a gidansu duk da horon da Abbanta ya yi mata ta hanyar jibga mata duka aikin gidan gaba ɗaya.
Bayan wani ɗan lokaci aka masu sulhu ta koma gidan mijinta, tun daga lokacin take taka-tsan-tsan da duk wani abu da zai sosawa mijin rai, ƙazantar ce dai taka sa dainawa har zuwa wannan lokacin.
Ko da yake mijinta kullum idan ya fita kasuwa tun safe baya dawowa sai wuraren goma na dare, in ya yi sauri ne yake dawowa tara. Wannan abun ya taka muhimmiyar rawa gurin ƙara lalacewarta da yin duk abinda ta ga dama a cikin yini, sai lokacin dawowarsa ya gabato take nutsuwa.
Su Sagira da Hanifa sun kasance ƙawayenta tun lokacin da ta dawo unguwar da zama dalilin da ya sanya kenan har bayan aurenta ta kasa rabuwa da su. Kasancewar gidanta a cikin unguwa ya sanya suka maida gidan dabdalarsu, ko hira zasu yi da samarinsu cikin gidan suke zuwa. Idan sun samu alkhairi sai su sammata, girke-girke suke kala-kala idan sun yi rarar kuɗin samari duk a gidan...
Yawon biki kuwa ko amara ƙirjin biki ta shafa mata lafiya.
managarciya