Kungiyar Middle-Belt Patrotic Congress (MBPC) ta yi zargin wani makirci da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ke yi don amfani da kudade daga CBN don neman shugabancin kasa.
Kungiyar, yayin bayyana hakan a wurin taron manema labarai a Abuja a ranar Lahadi, 17 ga watan Disamba, ta ce a halin yanzu El-Rufai na neman goyon bayan manyan mutane daga arewa a kokarinsa na kawo cikas ga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Garba Jacob, shugaban kungiyar, ya yi nuni da cewa Bello Mohammed El-Rufai, shugaban kwamitin dokokin kula da bankuna, na cikin shirin yin amfani da CBN don samar da kudin yin aikin takarar shugabancin kasa na El-Rufai.
Sanarwar ta ce: "Mun lura cewa el-Rufai, bisa halinsa, ya shirya yadda za a samu kudi domin wata kasuwanci nasa mai alamar tambaya, da ya ke boyewa karkashin kamfanin hannun jari, Afri-Venture Capital Company Limited, wacce za ta fara aiki a 2024, da $100 miliyan, fiye da N100 biliyan da zai yi amfani da shi don siye matasa, mafi yawanci matasan musulmi a matsayin wani mataki na ware kiristoci.
"Mun fahimci cewa matasan da ake tarawa da sunan koya musu sana'a, amma daga bisani za a yi amfani da su ne don zanga-zanga da za ta tsayar da kasa cak duk lokacin da el-Rufai ke bukata."
Kungiyar ta yi ikirarin cewa matsayin dan El-Rufai wata hanya ce da za ta bai wa mahaifinsa damar juya dukiyar Najeriya ta hanyar babban bankin kasa.
Sun yi ikirarin cewa wannan damar da ya ke da shi za ta shafi tattalin arziki, suna gargadin abin da ka iya faruwa idan ya fito neman takarar shugabancin kasa a 2027.
Hakazalika, kungiyar ta yi kira ga shugabannin arewa, ciki har da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da Janar Badamasi Babangida, su yi takatsantsan wurin harka da El-Rufai don tabbatar kasa ta zauna lafiya.