Manir Dan'iya Ba Zai Yi Takarar Gwamnan Sakkwato Ba?

Manir Dan'iya Ba Zai Yi Takarar Gwamnan Sakkwato Ba?

 

Mataimakin Gwamnan Sakkwato Honarabul Manir Muhammad Dan'iya da yawan mutane a jihar Sakkwato sun yi hasashen zai yi takarar gwamnan jihar Sakkwato bayan kammala wa'adin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ganin yanda ya zama na biyu a tsarin mulkin jiha wanda ke jan ragamar kula da ma'aikatar kananan hukumomi a tun sanda gwamnatinsu   ta fara kusan shekara bakwai da suka gabata.

A 2019 jam'iyar PDP ta tsayar da shi takarar gwamna kafin daga baya ya janye takararsa ga Gwamna mai ci, wannan danawar da ya yi ta sanya wasu ke ganin ba makawa sai ya yi takarar gwamna a 2023.
Da yawan mutane sun yi hasashen mataimakin gwamnan zai zama sahun gaba ga sayen fom na takarar gwamna a duk sanda aka fara sayarwa, ana danganta shirinsa yafi saboda duk wanda zai sayi fom a jihar don ya tsaya takarar gwamna bai kai girman mataimakin gwamnan ba.
Managarciya tana biye kwamishinan muhali Sagir Attahiru Bafarawa da tsohon mataimakin gwamna Barista Mukhtari Shagari sun sayi fom na neman takarar gwamna kuma sun bayyanawa  al'ummar jihar Sakkwato, za su yi takarar.
Bayan wadan nan ba wani bayani na fili ga sauran masu neman tikitin takarar gwamna a PDP kan sun saye fom sai dai kawai an ce-an ce.

Saura kwana uku kacal PDP ta rufe sayar da fom a sabon lokacin da ta sake bayarwa, kan haka muke ganin shin ko Mataimakin gwamna  ba zai shiga zabe ba a wannan marar, ko kuma wayo da nuku-nuku ne suke ta yi har ya kawo suke 'yar tsere da lokaci.
A tambayar da muka yi wa wani makusancinsa kan yaushe zai sayi fom ko ya saya ya ce gaskiya shi bai san abin da ake ciki ba kan maganar fom.
Daraktan yada labarai a ofishin mataimakin gwamna Aminu Abdullahi ya ce ba yanzu ne yakamata su yi magana ba a bari sai bayan wa'adin sayar da fom ya cika.

"zuwa yanzu ba wata magana na an  saye ko ba za a saye ba, ana nan ana jira tun da ba a rufe ba, in an rufe duk bayanin da za a yi a ranar za a yi shi", a cewarsa.