Mambobin Jam'iyar APC Ba Su Da Hurumin Kai Kararta, Babban Taronta Ya Gudana Kamar Yadda Aka Shata--Kotu

Mambobin Jam'iyar APC Ba Su Da Hurumin Kai Kararta, Babban Taronta Ya Gudana Kamar Yadda Aka Shata--Kotu

 

Wata babbar kotu a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya ta yanke hukuncin kyale jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta gudanar da babban taronta na kasa a ranar 26 ga watan Maris na wannan shekarar.

 

A ranar Juma'a alkalin kotun, Mai shari'a Bello kawu ya yanke hukunci cewa 'ya'yan jam'iyyar ba su da hurumin kai kararta.
 
Ya ce wani umarnin Kotun Kolin Najeriya kan wani batu irin wannan ya sha gaban wanda babbar kotun ta fitar na 18 ga watan Nuwambar bara.
 
Kotun ta daga zamanta zuwa ranar 30 ga wannan watan na Maris domin ci gaba da sauraren karar.
 
Wani mamba a jam'iyyar mai suna Salisu Umoru ne ya shigar da kara inda yake so kotun ta hana jam'iyyar ta APC da gwamna Mai Mala Buni da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC su shirya babban taro na kasa na jam'iyyar har sai bayan an kammala sauraren karar da ya shigar.
Kafin wannan hukuncin ana ta shakku da hasashen ganin kamar taron ba zai gudana ba kamar yadda aka shata, saboda maganar na gaban kotu.
An yi ta sanya ranar gudanar da taron domin a zabi shugabannin jam'iyyar amma ana dagawa, hakan ya sanya wasu ke ganin kamar za a sake yin abin da aka saba ne.