Ayyukan Raya Mazabu: Hon. Lawan Shettima ya yiwa al'umma mazaɓarsa goma ta arziki a jihar Yobe
Daga Muhammad Maitela, Damaturu.
A qoqarinsa na kyautatawa al'ummar mazavarsa, domin inganta rayuwa da bunqasa tattalin arzikin yankin, xan Majalisa mai makiltar qananan hukumomin Geidam, Bursari da Yunusari a zauren Majalisar Wakilai ta Tarayya, Hon. Lawan Shettima Ali (Yashi) wanda tun bayan kasancewarsa a Majalisar, yake gudanar da muhimman ayyukan ci gaban yankin, tare da raya yankin sakamakon irin yadda aka fuskanci matsalar tsaron da ta xaixaita al'amurra da qalubale kala-kala ga jama'a.
A farkin wannan makon a garin Gaidam a jihar Yobe, Hon. Shettima ya yiwa al'ummar mazavarsa goma ta arziki, inda ya qaddamar da raba kayan tallafin da suka dace da al'ummar wannan mazava tare da samar da mafita dangane da qalubalen da ake ciki sakamakon matsalar tsaron Boko Haram wanda ya jefa jama'a cikin mawuyacin hali. An samar da waxannan kayayyakin tallafi domin sake farfaxo da yankin wanda ya qunshi kayan noma, sana'o'in hannu, kiwon lafiya, ilimi da tallata wa vangaren naqasassu a yankin.
Waxannan kayayyakin tallafi na musamman, domin sake farfaxo da ci gaban al'ummar waxannan qananan hukumomi, sun haxa da motocin xaukar maras lafiya guda 3 (Equipped Ambulances), motoci 4 qirar 'Gulf Wagon', mashina masu bodi15 (Jega), Keke Napep 35, injinan markax 77 domin mata, injinan noman rani 350, kekunan guragu 65 domin taimaka wa naqasassu, kekunan xinki ga 330, shanun noma da amalanke da garman noma 62, kayayyakin karatun xalibai 31 tare da na'urorin komfuta (HP Laptops) ga makarantu guda biyar a yankin, sai buhunan shinkafa 600 (25kg) da buhunan hatsi 600 (25kg) da sauran su.
Da yake jawabi a lokacin raba waxannan kayayyakin, Hon. Lawan Shettima ya bayyana cikakkiyar godiyarsa ga Allah bisa bashi wannan dama ta yiwa al'ummar sa hidima, tare da sauke wani vangare na nauyin da Allah ya xora masa, a matsayin xan Majalisa mai wakiltar al'ummar yankin a zauren Majalisar Wakilai ta Tarayya. Haka kuma ya gode wa jama'ar yankin bisa cikakken goyon baya tare da qwarin gwiwar da suke bashi tun daga farko zuwa yanzu.
Bugu da qari kuma, Hon. Lawan Shettima ya jaddada wa al'ummar mazavarsa cewa zai ci gaba da gudanar da makamantan waxannan muhimman ayyukan alheri domin ci gaban yankin tare da inganta rayuwa da walwalar jama'a. Haka kuma ya bukaci jama'ar yankin da jihar APC baki xaya su ci gaba da marawa gwamnati baya a kowane mataki kuma ya nemi su zavi jam'iyyar APC a zave mai zuwa, ya ce duba da ayyukan alherin da gwamnatin jihar Yobe ta kawo a yankin da gwamnatin Tarayya a qarqashin shugaban qasa Muhammadu Buhari wanda ya bunqasa harkar tsaro aka samu zaman lafiya a jihar da Arewa Maso Gabas da qasa baki xaya.
"Wanda bisa ga wannan ne muke jaddada godiya da yabawa Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni da kuma qoqarin shugaban qasa Mohammadu Buhhari sakamakon ayyukan alherin da suka yi wanda ya taimaka al'ummar mu suka shaqi iskan yanci da zaman lafiya mai xorewa.” in ji Hon. Shettima.
Har wala yau, wannan muhimmin taron ya samu halartar manyan jami'an gwamnatin jihar Yobe, wanda suka haxa da wakilcin Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, halartar Kakakin Majalisar Dokokin jihar Yobe, Rt. Hon. Ahmed Lawan Mirwa tare da sauran yan masalisu, shugabannin qananan hukumomi na riqo, shugabannin jam'iyyar APC na qananan hukumomi tare da na gundumomi da dubban magoya bayan jam'iyyar APC a jihar.
Bugu da qari kuma, taron ya karvi dandazon shugabanin jam'iyyar PDP da sauran jam'iyyun adawa tare da xaruruwan magoya bayansu, waxanda suka sauya sheqa zuwa jam'iyyar APC. Waxanda suka bayyana gamsuwarsu bisa kyawawan manufofi da tsarin tafiyar gwamnatin jihar da muhimman ayyukan da Hon. Lawan Shettima ya aiwatar don ci gaban yankin baki xaya.
Haka zalika kuma, an gudanar da rarraba kayayyakin tallafin cikin nasara a baki xayan gundumomi 31 da ke cikin waxannan qananan hukumomi uku da ke mazavar. Wannan jama'a da dama suka bayyana gamsuwarsu bisa ga muhimman ayyukan raya mazavu wanda Hon. Lawan Shettima Ali ya ke aiwatar wa waxanda suka shafi kowane vangaren rayuwar al'umma. Inda kuma suka nanata cewa, waxannan kayayyakin tallafin za su taimaka wajen sake farfaxo da yanki daga mawuyacin halin da matsalar tsaron Boko Haram ya jefa yankin a ciki.
managarciya