Gwamnonin Nijeriya Da Ɗangote Da Otedola Suna Ganawa A Abuja

Gwamnonin Nijeriya Da Ɗangote Da Otedola Suna Ganawa A Abuja
Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, da sauran gwamnonin Najeriya, da Alhaji Aliko Dangote, Femi Otedola, da sauran manyan baki na halartar wani muhimmin taro na tattalin arziki a cibiyar ‘Yar’Aduwa da ke Abuja.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emiefele, da Kakakin Kungiyar Dattawan Arewa Hakeem Baba Ahmed, Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki, Tsohon Sakataren Tarayya Pius Ayim Pius, Tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda MD Abubakar, Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP Ahmed. Mu'azu, tsohon shugaban EFCC Nuhu Ribadu, Alhaji Abdussamad Isyaka Rabiu da sauransu.
Za a bayyana cikakken bayanin taron a karshen taron bayan an kammala.
Taro ne da zai mayar da hankali kan tattalin arziki.