Home Uncategorized Majalisa za ta cigaba da goyon bayan jami’an tsaro don  su cimma...

Majalisa za ta cigaba da goyon bayan jami’an tsaro don  su cimma bukatar da suka sanya gaba—–Sanata Wamakko

8
0

 

Shugaban kwamitin tsaro a majalisar dattijai Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya ce kwamitin tsaro zai cigaba da bayar da goyon baya ga hukumomin tsaro don su cimma manufar da suka sanya gaba.

 

Sanata Wamakko ya yi wadannan kalamai ne a lokacin da ya jagoranci kwamtinsa a hidikwatar tsaro ta kasa dake Abuja  ya ce la’akari da kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta a halin yanzu suna tabbatarwa hukumar tsaro da ta leken asiri goyon bayan kwamiti har a cimma bukatar da aka sanya a gaba.

 
Sanata Wamakko ya damu kwarai ga matsalar tsaron kasar nan musamman a yankin arewa maso yamma da jihar Sakkwato kanta, kan haka a koyaushe yake ta fadi tashi da goyon bayan jami’an tsaro domin ganin al’umma sun samu zaman lafiya musamman a yankin sakkwato ta gabas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here