Gwamnan Katsina  Ya Dauki Malamai 7,325 Aikin Gwamnatin Jiha 

Gwamnan Katsina  Ya Dauki Malamai 7,325 Aikin Gwamnatin Jiha 

 

Gwamna Umar Dikko Radda, ya mika takardun kama aikin din-din-din ga sabbin malamai 7,325 da aka dauka aiki a gwamnatin jihar Katsina. 

Gwamnan wanda ya taya malaman murna, ya bukaci su kasance masu yin aiki tukuru kasancewar koyarwa tamkar jahadi ne saboda Allah.
Ya ce Allah ne ya ba su wannan aikin don yi wa al'umma hidima, don haka su kasance malamai masu aiki da tsoron Allah da kuma koyarwa bisa gaskiya, rahoton Leadership. 
"Allah ne ya zabe ku, kar ku ci amanarsa. Ku yi abin da ya dace kuma kar ku ci amanar jihar ku, ba zamu iya yi maku hisabi ba, amma Allah na jiran kowa a madakata. 
Gwamnan ya kara da cewa ma'aikatar ilimi na samun sauye-sauye a jihar, don haka akwai bukatar sabbin malaman su zage damtse don bunkasa harkar ilimin jihar. 
Gwamna Radda ya kuma yi alkawarin horas da sabbin malamai kafin tura su wuraren da za su aiki, inda ake sa ran za su kama aiki a ranar 6 ga watan Janairu, 2024.