Daga Muhammad Maitela, Damaturu
A kokarin bunkasa harkokin jindadi da walwalar al'umma tare da bunkasa harkokin tattalin arziki, gwamnatin jihar Yobe ta bayyana cewa ta kammala ayyuka 133 daga cikin 160 na samar da wutar lantarki a birane da karkara- kana da kaddamar da karin sabbin ayyuka 27 wadanda ke ci gudana a halin yanzu.
Wannan bayanin ya fito ne daga Babban Manajan Hukumar Raya yankunan karkara da Wutar Lantarki ta jihar Yobe (REB), Engr. Umara Mustapha a lokacin da yake yi wa manema labaru karin haske dangane da ayyukan Hukumar, a Sakatariyar NUJ da ke Damaturu, a karshen mako.
Mustapha ya ce, gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Mai Mala Buni, ya ce hukumar ta sada yankunan karkara da wutar lantarki tare da girka na'urorin rarraba wutar lantarki mai karfin KV 33 a garin Buni Yadi, sayo injinan bayar da wutar lantarki samfurin KVA mai lamba 2 No 250 a asibitin koyarwa na jami’ar jihar Yobe dake Damaturu, da karin inji mai karfin KVA 100 domin Yobe ICT a ofishin Gwamna. Sannan da gyare-gyare tare da bunkasa layin 33 kV a kananan hukumomin Damaturu, Babbangida, Bayamari, Gaidam, Dapchi da Yunusari a jihar.
Babban Manajan Hukumar ya kara da cewa, sauran ayyukan da suka aiwatar a fadin jihar sun hada da samar da kananan tashoshin rarraba wutar lantarki tashar 2 masu karfin 500 KVA, fadada TDN da gina sabbin layukan KV 33 a Yotcho dake karamar hukumar Potiskum.
“Sauran sune sanya layukan wuta a garin Arfani na karamar hukumar Jakusko, garin Aji Dawari a Bursari da wutar lantarki Wachakal, Shekau, Dumsa, Makera, Dumuwal, Kasaisa, Garin Mallam Adamu duk a jihar Yobe." in ji shi.
Har wala yau kuma ya sake bayyana cewa, gwamnatin jihar Yobe ta samar da karin wasu kayayyakin wutar lantarki a garuruwa 26 a kananan hukumomi 17 dake fadin jihar, a karkashin shirin gina gidajen da gwamnatin jihar ta ke gudanarwa.