Daga Aminu Amanawa, Sokoto.
A wani aikin tallafawa al'ummomin da yake makwabtaka da su, kamfanin siminti na BUA ya samar da rijiyar burtsatse waton Borehole mai amfani da hasken rana ga al'ummar kauyen Dagelawa daya daga cikin kauyukkan dake makwabtaka da kamfanin siminti na BUA dake jihar Sakkwato.
Da yake magantawa yayin hannun ta rijiyar ga al'ummar, jami'in hulda da jama'a na kamfanin Sada Suleiman ya bayyana cewa samar da rijiyar mai daukar galan dubu 10 da za ta yi aiki da hasken rana ba ruwansa da wutar NEPA kamfanin simintin ya yi ne da manufar ragewa al'ummar kauyen wahalhalun da suke fama dashi na neman ruwan sha domin amfanin su.
"Kamfanin simintin ya yanke shawarar samar da rijiyar ne a wani mataki na bada tashi gudunmawa ga al'ummar kauyen Dagelawa, domin suma su amfana da shiraruwan tallafawa al'umma da kamfanin ke yi, inji shi".
Ya ce aiyukkan da suka gabatar guda biyu sun lakume kudi miliyan 25, miliyan 15 a wurin gina bohol, miliyan 10 a wurin magani ga asibitoci 8 dake cikin gundumomin Wamakko don ragewa marasa lafiya radadin rashin kudin magani.
Da yake karbar rijiyar burtsatsen ta Borehole a madadin al'ummar kauyen Uban kasar Wajeke Abubakar Mailato Gumbi ya bayyana jin dadin sa kan karimcin kamfanin.
"A madadin al'ummar wannan kauyen mun ji dadi matuka kan karancin da kuka nunawa al'ummar wannan garin na samar masu da hanyar samun ruwan sha mai amfani da hasken rana, wannan abin a yaba ne, mun gode kuma zamuyi kokari wajen amfani da ita yanda yakamata inji uban kasar.
Ko baya ga wannan ma kamfanin siminti na BUA ya bayar da magunguna kyauta ga kananan assibitoci 8 na karamar hukumar mulkin Wamakko da mazaunin kamfanin yake kusa da su.
Assibitocin da suka amfanan kuwa sun hadar da Assibitin Gidan Bailo, Mobile Police clinic, Bakin Kusu da kuma assibitin Gidan Boka.
Sauran Assibitocin sun hadar da assibitin garin Kalambaina, Wajeke, Sabon Garin Alu da kuma arkilla.
Da yake nuna godiya da jin dadin sa kan tallafin, mataimakin shugaban ƙaramar hukumar ta Wamakko Zubairu Muhammad Dundaye, ya bayyana cewa wannan kari ne da kokarin da kamfanin keyi lokaci zuwa lokaci a karamar hukumar.
Adon hakane ya bukace su da suyi amfani da kayan domin amfanin su, inda kuma ya bukaci kamfanin da ya dore da hakan domin amfanin al'ummar ƙaramar hukumar.