An Shiga Matsin Lamba, Gwamnoni Sun Karbo Bashin N46.1bn Domin Biyan Albashi

An Shiga Matsin Lamba, Gwamnoni Sun Karbo Bashin N46.1bn Domin Biyan Albashi

 

Wasu gwamnatocin jihohi sun karbo aron kusan N46.17bn daga bankuna uku tsakanin Janairu zuwa Yunin shekarar nan ta 2023. 

Binciken Punch ya ce rahotonnin rabin shekara da aka samu daga bankunan Access, Fidelity da Zenith ya nuna jihohi sun karbo bashin kudi. 
Gwamnonin kasar sun fi dogara ne da bankin Access wajen cin bashi a shekarar nan, inda a cikin watanni shida su ka ba jihohi aron N42.97bn. 
Bankin Zenith ya bada aron N1.78bn sai jihohi su ka ci bashin N1.42bn daga bankin Fidelity. 
Rahoton ya ce a cikin jihohi 36 da ake da su a kasar nan, ba a samu bayanai a kan jihohi irinsu Ribas, Sokoto, Akwa Ibom, Edo da Legas ba. 
Sauran jihohin da babu bayanai game da kudinsu daga farkon shekarar bara zuwa bana su ne: Kaduna, Bauchi, Zamfara, Yobe da kuma Ogun. 
Alkaluman da aka samu na jihohi 25 ya nuna gwamnonin sun yi harin samun N219.56bn a farkon 2023, amma a karshe N182.26bn aka iya samu.