Tambuwal Zai Yi Garambawul Ga Jami'ansa Masu Kula Da Harkokin Yada Labarun Gwamnati

"Masu baiwa gwamna shawara ina ganin in ka cire shugaban karamar hukumar Sakkwato ta arewa da yake ciyaman a yanzu akwai makamantansa su shidda, su Yusuf Dingyadi(Senior Special Assistance) ne na gwamna kan sha'anin yada manufofin gwamnati sun kai su shidda, ban da kananan S.A dake Social Media, ban da kwamishinan yada labarai da mai watsa labarai a fadar gwamnati, ban da Abu Shekara wanda shi aikinsa wayarda kan jama'a, Wannan kalubale ba nawa ba ne ni kadai, jama'a sun ce ba ku aiki, in ba ku aiki zan yi maku garambawul ni kuma." Tambuwal ya tabbatar da hakan gaban magoya bayan PDP.

Gov. Tambuwal

Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya sha alwashin yin Garambawul ga jami'ansa dake kula da harkokin yada labaran gwamnati domin ba su aikin da yakamata su yi.

A wurin taro Tambuwal ya furta cewa matukar aka rika tafiya haka gwamnatinsa ta zama ta kurame dole ya dauki mataki, "Abin mamaki nan shi ne bana iya tuna gwamnatin da ta baiwa ‘yan jarida aiyukka kamar wannan gwamnati, 'yan jarida wadanda aikinsu na jarida ne, da kwamishinoni da manyan sakatarori da manyar daraktoci duka akwai 'yan jarida cikinsu.

"Masu baiwa gwamna shawara ina ganin in ka cire shugaban karamar hukumar Sakkwato ta arewa da yake ciyaman a yanzu akwai makamantansa su shidda, su Yusuf Dingyadi(Senior Special Assistance) ne na gwamna kan sha'anin yada manufofin gwamnati sun kai su shidda, ban da kananan S.A dake Social Media, ban da kwamishinan yada labarai da mai watsa labarai a fadar gwamnati, ban da Abu Shekara wanda shi aikinsa wayarda kan jama'a, Wannan kalubale ba nawa ba ne ni kadai, jama'a sun ce ba ku aiki, in ba ku aiki zan yi maku garambawul ni kuma." Tambuwal ya tabbatar da hakan gaban magoya bayan PDP.

Ya kara da cewar "Olisa Metuh da ya zo jihar nan ya ce Gwamna Nijeriya ba ta san kana aiki ba, bai yiwu mutane su taru kan magana guda a ce kan kuskure suke ko dai ku gyara ko niko na gyara ku," Tambuwal ya hakikance kan yin garambawul.