Duk Ministan da ya ƙi amsa gaiyatar mu sai ya bar gwamnatin Tinubu - Akpabio

Duk Ministan da ya ƙi amsa gaiyatar mu sai ya bar gwamnatin Tinubu - Akpabio

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya shaidawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu cewa ministocin da suka ki girmama gayyatar majalisar kasa ba su da gurbi a gwamnatinsa.

Akpabio ya yi magana ne a yayin wani zama na hadin gwiwa na Majalisar Dokoki ta kasa inda Tinubu ya gabatar da kudirin kasafin kudin 2025 na Naira Tiriliyan 49.7 a jiya Laraba.

Akpabio ya ce Majalisar Dokoki ta kasa alama ce ta dimokuradiyya, yana mai jaddada cewa kin girmama gayyatar da wasu ministocin ke yi mata ya nuna cewa su ba 'yan dimokradiyya ba ne.

"Su (Ministoci) su sani cewa gayyata na ciki dokokin tsarin mulki kuma muna da ikon da tsarin mulki ya ba mu damar daukar wani mataki idan sun ki bayyana.

"Mu na kira ga shugaban kasa da ya gargadi wasu daga cikin ministocin da ba sa girmama wannan majalisa mai albarka," in ji Akpabio.