Nadin Garkuwan Kabin Argungu Ya Yi Armashi Matuka

Nadin Garkuwan Kabin Argungu Ya Yi Armashi Matuka
Garkuwan Kabin Argungu

 

Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto. 

 

An nada Shugaban Hukumar Rarraba Wutar Lantarki ta Kaduna, Engr. Garba Haruna a matsayin ‘Garkuwan Kabi’ ran jimua, 5 ga watan Nuwamba.

Mutane da dama ne suka halarci wannan biki, daga cikinsu akwai Shugaban Kasar Najeriya wanda Ministan Shari’ah Abubakar Malami ya wakilta, Shugaban Majalisar Dattijai Ahmad Lawan, Shugaban Masu Rinjaye Yahaya Abdullahi, Gwamnonin, Kabi, Sakkwato, da Zamafara, masu ci yanzu da wayanda suka shude, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, Sarakunan Zamfara, Maradun, Anka da sauransu duk sun samu zuwan wannan biki.

Kafin nan, amfara da addu’o’in taya murnar cika shekara ishirin da biyar saman karagar mulki na Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammad Mera, CON. Addu’o’in sun kunshi samun zaman lafiya, tsaro da cigaban yankin da najeriya baki daya.
Bayan haka, anyi daurin auren ‘yar Sarki wato Hajiya Habiba da Engr. Garba Haruna, a Masallacin Muhammadu Mera dake garin Argungu.
Hakazalika, bayan kammala daurin auren, anyi naddin sarautu kamar haka: Garkuwan Kabi (Engr. Garba Haruna) da na Ganuwan Kabi (Ahmad Lawan) da sauran su,
Bugu da kari, anyi wata yar kwarya kwaryar hawan darba, domin karrama wayanda aka nada.
Shi dai Garkuwan Kabi mutum ne mai son taimakawa jama’a, don ganin sun samu saukin rayuwa. Hakan ya sa, ya kirkiro Gidauniyar Tallafawa Jama’a a garin Argungu. Don haka wannan makami nashi ya cancance shi saboda kokarin da yake yi musamman wurin samarwa jama’a aikin yi. Inda wani maxaunin garin ke xwa yau munga mutane daban daban da suka zo taya mai martaba da Garkuwa murna ciki da wajen jihar.
Daga karshe, an kammala bukukuwan cikin lumana kuma manyan baki sun isa gidajensu lafiya. 

Kamar yadda 
Manajan
Gidauniyar Garkuwan Kabi  Malam  Bello Bishir  Musa, ya bayyanawa wakilin mu.