Sakkwato Na Cikin Jihohi Dake Kan Gaba A Yawan Yara Masu Fama Da Yunwa---Rahoto
Bisa ga alƙaluman binciken akwai akalla yara 297,832 a jihar dake fama da tsananin yunwa

Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa a shirye take domin daukan matakan da za su taimaka wajen rage yawan yaran dake fama da yunwa a jihar.
Mashawarcin gwamnan jihar Ahmed Aliyu kan harkokin cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a jihar Muhammad Bello ya sanar da haka a taron da aka yi domin SMART survey ta gabatar da sakamakon binciken yawan yaran dake fama da yunwa a jihohin Katsina, Sokoto da Zamfara a 2023.
Sakamakon binciken ya nuna cewa jihar Sokoto na daga cikin jihohin da suka fi yawan yaran dake fama da yunwa a Najeriya.
Bisa ga alƙaluman binciken akwai akalla yara 297,832 a jihar dake fama da tsananin yunwa.
Bello ya ce gwamnati za ta kirkiro matakan da za su taimaka wajen kawar da wannan matsala a jihar.
Ya kuma mika godiyarsa ga UNICEF kan mara wa gwamnati baya da take yi.
Daga nan Shugaban masana sinadarin inganta lafiya na UNICEF dake jihar Abraham Mahama ya ce talauci, rashin cin abincin da zai inganta garkuwar jiki da rashin tsaro na daga cikin matsalolin da ya sa jihar ke fama da yawan yaran masu fama da yunwa.
Mahama ya ce manoma da dama sun kasa noma gonakinsu saboda aiyukan ƴan bindiga da ake fama da shi a jihar.