Majalisar dokoki ta bayyana taikacinta kan halin da titunan birnin Sakkwato suke ciki

Majalisar dokokin jihar Sakkwato ta bayyana takaicinta kan halin da titunan birnin Sakkwato suke ciki, sun fashe da yin ramu da kuma tushewar wasu magudanun ruwa da kazanta dake saman hanyoyin kusan ko'ina.

Majalisar dokoki ta bayyana taikacinta kan halin da titunan birnin Sakkwato suke ciki

 A madadin majalisa jagoran 'yan majalisar APC Alhaji Bello Isah Ambarura ya sanar da matsayar majalisa kan titunan domin babu dadi da kwanciyar hankali ga masu ababen hawa dake birnin Sakkwato.

Haka ma ya ce sun karbi korafe-korafe ne a wuraren mutane kan halin da hanyoyin  ke ciki kan haka suka gayyaci wadan da lamarin ya shafa domin sanin hobbasar gwamnati ga kawar da matsalar da hanyoyin ke fama da ita tsawon lokaci.

Majalisar dokoki ta bayyana taikacinta kan halin da titunan birnin Sakkwato suke ciki

Mafiyawan shatale talen dake birnin jihar suna da ramu cikinsu sosai haka ma manyan titunan sun farfashe da suke bukatar gyara, wasu magudanun ruwa shara ta cika su, wasu titunan kuma shara ake zubawa samansu.

Majalisar dokoki ta bayyana taikacinta kan halin da titunan birnin Sakkwato suke ciki

Amadadin hukumomin gwamnati da majalisar ta yi wa gayyattar gaggawa Kwamishinan ma'aikatar filaye da gidaje na jiha Aminu Bala Bodinga ya ba da tabbacin gyara hanyoyin ba tare da jimawa ba domin har gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya ba da umarnin fitar da kudin aikin.