Dakarun Najeriya sun ceto waɗanda 'yanbindiga suka yi garkuwa da su a Kano
Dakarun rundunar Operation MESA, wadda ta kunshi jami’an Birgediya ta 3 ta Sojin Najeriya, tare da hadin gwiwar Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da ’Yasandan Najeriya, sun ceto mutane uku daga cikin biyar da aka sace a kauyen Lakwaya da ke karamar hukumar Gwarzo a Jihar Kano.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa wasu ’yanbindiga da ake zargin ’yan ta’adda ne sun kai wani sabon hari a garin Lakwaya, inda suka sace mutane biyar.
Da yake zantawa da Daily Trust, Kyaftin Babatunde Zubairu, Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Sojin Kasa , Birgediya ta 3, ya ce, “ya zuwa yanzu mun samu nasarar ceto mutane uku.”
A cewar majiyoyin yankin, lamarin ya faru ne a daren Lahadi a kauyen Zurin Mahauta, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba da tashin hankali.
Dagacin Zurin Mahauta, Murtala Mai Unguwa, ya bayyana cewa maharan sun mamaye yankin ne cikin dare, inda suka yi awon gaba da mutanen zuwa wani wuri da ba a sani ba.
managarciya