Tsaro: Gwamnan Kano zai samar da Jiragen Sintiri marasa matuka
Gwamna Yusuf zai samar da Jiragen Sintiri marasa matuka da kayan aiki don magance rashin tsaro a kan iyakoki
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana shirin gwamnatin jihar na samar da jiragen sintiri na zamani (drones) da sauran kayan aikin tsaro domin sa ido da gaggawar daukar mataki, don kare al’ummar da ke zaune a yankunan kan iyaka tsakanin Kano da Katsina.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce Gwamnan ya yi wannan bayani ne yayin da yake duba yadda Rundunar Hadin Gwiwa (JTF) ta shirya wajen fuskantar hare-haren ’yan bindiga da suka faru a sansanoninsu uku da ke Tsanyawa da Shanono a ranar Talata.
Gwamnan ya roki al’ummar yankunan da abin ya shafa da su taimaka wa JTF da bayanai masu amfani game da motsin ’yan bindiga.
Gwamna Yusuf ya bayyana cewa lokacin da ya kai ziyarar neman goyon baya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan lamarin, shugaban kasar ya amsa buƙatar cikin gaggawa.
Ya umarci JTF da su ba da himma wajen kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su a Tsanyawa da Shanono daga hannun ’yan bindiga.
"Mun san cewa sun dade suna kai hare-hare a kan al’ummomin da ba su ji ba ba su gani ba, musamman a nan Tsanyawa da Shanono. An rasa rayuka da dama, kuma an yi garkuwa da mutane da yawa."
“Na tabbatar muku, da ikon Allah, wadanda aka sace za a dawo da su cikin iyalansu,” in ji shi.
managarciya