An Samu Musulmin Farko Da Ya Fara Fassara Al-Qur'ani Cikin Harshen Koriyanci 

An Samu Musulmin Farko Da Ya Fara Fassara Al-Qur'ani Cikin Harshen Koriyanci 
 

Daga Barr. Nuraddeen Isma'eel 

 

Dakta. Sahib, Shine malamin Addinin Musulunci a Kasar Koriya na farko Wanda ya Fara fassara Al-Qur'ani Mai girma Zuwa harshen su ta Koriyanci.

 
Daktan; Ya shafe Shekaru bakwai cif Yana wannan aikin na fassara, bisani bashi da Wani wuri na idan ya tashi wannan aikin na fassara Sai a babban masallacin Kasar Dake kasar Koriyan.
 
Bugu da Kari, bayan da Daktan ya kammala fassaran. sai ya damka littafin na Al-Qur'anin Mai girma ga Sarkin Saudiya wato Fahad a domin ya kaddamar da wannan littafin.
 
An shaida Mana cewa! Dakta Sahid ya wallafa wasu littafan Addinin Musulunci da Daman gaske inda duk yayi su da harshen su ta Koriyanci a domin isar da Sakon Addinin Musulunci.
 
Yaren Koriyanci dai aƙalla Sama da mutane miliyan 80 ne ke jinsa a fadin Sassan duniya.