Cire Hijabi: Zanga Zanga Ta Barke kan Cin Zarafin ’Yan Matan Shi’a a Abuja 

Cire Hijabi: Zanga Zanga Ta Barke kan Cin Zarafin ’Yan Matan Shi’a a Abuja 

Daruruwan 'yan shi'a ne suka fantsama titunan Abuja domin nuna rashin jin dadi kan cin zarafinsu. Yan kungiyar sun nuna damuwa kan yadda yan sanda suka cirewa mambobinsu mata hijabi a Abuja.

AIT ta wallafa faifan bidiyon da yan shi'an ke zanga-zanga wanda mafi yawansu mata ne.
Wata mai suna Fatima Ibrahim, mai magana da yawun masu zanga-zangar ta caccaki jami'an tsaro kan lamarin. Fatima ta ce hijabi addini ne da al'ada kuma 'yancinsu ne wanda bai kamata a ci zarafinsa ba. Ta ce tube musu hijabi da cin zarafinsu yafi zafi a gare su fiye da harbinsu da alburusai.
"Mun zo nan ne domin fadawa jami'an tsaro cewa mun yi Allah wadai da abin da suka aikata." "Muna son fadawa dukan Musulman duniya su yi duba ga wannan abu da yan sanda suka aikata." "Hijabi dokar Allah ne wanda ya halicci sammai da kasai kuma ubangijin talikai." - Fatima Ibrahim 
A wani labarin, kun ji cewa wasu yan ta'adda da ake zargin yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari kan makarantar Shi'a ta Faudiyya a Yobe. 
Rahotanni sun nuna cewa yan ta'addar sun kai hari ne cikin dare a lokacin da dalibai ke cikin barci a makarantarsu da ke jihar. Rahoto ya nuna cewa lamarin ya faru ne a makarantar Faudiyya da ke karamar hukumar Geidam kuma an samu harasar rayuka.