Sanata Lamido Yayi Ta’aziya Ga Mutanen Garu A Sakkwato
Sanata Ibrahim Lamido ya yi ta’aziyar rasa mutane 10 da aka yi da kuma jajantawa wadanda suka samu rauni a garin Garu dake cikin karamar hukumar Illela a jihar Sakkwato.
Sanata Ibrahim Lamido a sakon da ya aikawa al’ummar garin ta hannun ofishin yada labaransa ya bayyana kaduwarsa da yanda ‘yan bindigar suka shiga garin suka yi wannan ta’addancin a lokaci mafi tsada ga jama’ar musulmi.
Sanata Lamido ya bukaci muatnen garin su dukufa ga rokon Allah ya kawar da lamarin domin komai mai sauki ne a wurinsa.
Ya nemi su kwantar da hankalinsu gwamnatin Sakkwato karkashin Ahmad Aliyu Sokoto na kan kokarin ganin an kawar da batagari a jiha baki daya, sai dai wannan buri ba zai cika ba sai da hadin kan mutane domin da dan gari an ka ci gari.
Sanata ya kara jaddada cewa alkawalin da suka dauka na samar da tsaro a yakin gaba daya ba za su taba yin sanyi ba har sai an cika alkawalin, da fatar dai mutane za su ci gaba baiwa gwamnati hadin kai wurin samun bayanan sirri.
A ranar Assabar data gabata ne wasu 'yan bindiga dauke da miyagun makamai suka shiga garin Garu suka kashe mutum 10 tare da jikkata mutane da dama.
managarciya