Ba Zan Iya Sanya Rayuwata Cikin Haɗari Ba----Shaikh Gumi Ya Yi Watsi Da 'Yan Bindiga
Daga Abdul Dan Arewa
Babban Malamin addinin Musulunci da ke zaune a Kaduna, Sheik Ahmad Gumi, ya ce ba zai sake yin mu'amala da ƴan bindiga ba har sai "al'amuran siyasa sun canza."
Gumi ya ce tunda gwamnatin tarayya ta ayyana su a matsayin ƴan ta’adda, ba zai sake yin wata hulda da su ba.
"Ba zan so in sake jefa kaina ga haɗari ba kuma in sanya haske a kaina ba dole ba. Na yi duk abin da zan iya yi don na yi wa al’umma gargaɗi a kan hanya mafi dacewa don yin hakan, amma da alama shawarata ta yi kunnen uwar shegu,” inji shi.
Da yake magana a wata hira da Jaridar Premium Times, malamin ya ce ya jefa rayuwarsa cikin hadari domin zaman lafiya a kasar nan ta hanyar zuwa dajin domin hada ƴan bindigar duk da irin kallon da suke yi masa.
Ya kara da cewa, “Yana da hadari, amma duk da haka mun yi kasada da rayukanmu don ganin mun samar da zaman lafiya a wannan kasa. Dole ne wani ya dauki wannan kasadar, muka dauka, muka kuma gode wa Allah da ya sa muka fito lafiya da ilimi, da sanin yadda za a yi a kan wannan lamari.
"Watakila a nan gaba idan yanayin siyasa ya canza zuwa mafi kyau, za mu iya sake yin hakan domin a samu zaman lafiya, zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar."
managarciya