Rikicin siyasa da ya sako APC a gaba a jihar Sokoto ya canja salo bayan magoya bayan Sanata Ibrahim Lamido sun yi martani kan kalaman na hannun daman Sanata Aliyu Wamakko.
Sun dura a kan da shugaban tsagin jam’iyya na jihar, Isa Sadiq Achida a kan bayyana shakku a game da ingancin siyasar Sanata Ibrahim Lamido da zamansa dan asalin Sakkwato.
Daily Trust ta wallafa cewa a wata sanarwa da suka fitar, magoya bayan Lamido sun ce zarge-zargen da ake masa abun dariya ne, kuma ana yinsu ne saboda tsantsar tsoro.
Magoya bayan sun bayyana Sanata Ibrahim Lamdo da cewa ba wai kawai ɗan siyasa ba ne, amma ɗan asalin gidan Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo ne, wanda ya kafa Daular Sakkwato.
Sanarwar ta ce: “Tambayar asalin Lamido kamar raina jinin da ya kafa wannan jiha ne." Sun kuma bayyana cewa hare-haren da Wamakko ke kai wa kan Lamido na da alaƙa da tsoron farin jinin matashin ɗan siyasar da kuma rashin iya sarrafa shi.
Da aka nemi jin ta bakinsa, Isa Sadiq Achida ya dage cewa Lamido ba ɗan asalin jihar Sakkwato ba ne, yana mai cewa ba za a ba shi dama ya tsaya takara a ƙarƙashin APC a 2027 ba.
“A matsayinsa na wanda ya soki Sanata Aliyu Wamakko da karya hadin kan jam’iyya, ba zai samu tikitin APC a Sokoto ba."
Achida ya ƙara da cewa lokaci ya wuce da baƙi ke cin moriyar arzikin mutanen Sakkwato don samun nasarar siyasa.
Sai dai magoya bayan Lamido sun ce: “Sanata Lamido ba ya buƙatar amincewarku don ya ci gaba da buga siyasa."
Rahotonni sun bayyana cewa wannan rikicin ya raba kan sarakunan gargajiya a jihar, inda wasu ke goyon bayan bangaren Lamido yayin da wasu suka tsaya a gefen Wamakko.
A baya, mun wallafa cewa ana kara samun rabuwar kai a tsakanin jiga-jigan jam’iyyar, musamman Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da Sanata Ibrahim Lamido a Sakkwato.
Duk da cewa APC ta samu gagarumar nasara a jihar a zaben 2023, nasarar ba ta hana barkewar rikici ba wanda ke kara tsananta a cikin jam’iyya a tsakanin manyan 'yan siyasan biyu.
Jam’iyyar APC a Sakkwato ta dare gida biyu sabida sabanin da aka samu, inda aka samu bangaren da Sanata Aliyu Wamakko ke jagoranta da kuma na Sanata Ibrahim Lamido.