Bafarawa Da Lamiɗo Da Gusau Tare Da Wasu Mutum 34  Ne Za Su Yanke Hukunci Kan Shugaban Ƙasa A PDP

Bafarawa Da Lamiɗo Da Gusau Tare Da Wasu Mutum 34  Ne Za Su Yanke Hukunci Kan Shugaban Ƙasa A PDP

Shugabanin PDP sun zaɓi gwamnoni uku  Samuel Ortom (Benue), Darius Ishaku (Taraba) da Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu) mambobi a cikin mutane 37 da su yanke hukuncin karɓa-karɓa da yankin da ɗan takarar shugaban ƙasa zai fito a jam'iyar PDP domin tunkarar zaɓen 2023.

Kwamitin zai fitar da yankin da za a raba manyan muƙaman gwamnati in an samu nasara.
Sakataren tsare-tsare na ƙasa Umar Bature ne ya fitar da sunayen da suka haɗa da tsoffin gwamnoni  Ayo Fayose (Ekiti), Sule Lamido (Jigawa), Ahmed Makarfi (Kaduna), Liyel Imoke (Cross River), Boni Haruna (Adamawa), Ibrahim Dankwabo (Gombe), Ibrahim Shema (Katsina), Ibrahim Idris (Kogi) Attahiru Bafarawa (Sokoto) da Jonah Jang (Plateau).

Sauran su ne  Tom Ikimi (Edo), Mao Ohuabunwa (Abia),
Emmanuel Ibokessien (A/Ibom),
Prof. A. B. C. Nwosu (Anambra)
Senata Abdul Ningi (Bauchi), Boyelayefa Debekeme ( Bayelsa) da Sanusi Daggash (Borno).
Jagoran marasa rinjaye a majalisar waƙillai Ndudi Elumelu (Delta), Amb. Franklin Ogbuewu (Ebonyi), Mohammed Abdulrahman (FCT), Chief Fidelis Izuchukwu (Imo),
Amb. Aminu Wali (Kano), Kabiru Tanimu Turaki, SAN (Kebbi) da Kawu Baraje (Kwara) dukkansu suna cikin sunayen.
Haka kuma akwai Chief Olabode George (Lagos), Mike Abdul (Nasarawa), Prof Jerry Gana (Niger),
Hon. Daisi Akintan (Ogun), Dr. Omotayo Dairo (Ondo), Prof. Adewale Oladipo (Osun), Sen. Hosea Ayoola Agboola (Oyo), Austin Opara (Rivers), Adamu Maina Waziri (Yobe) da tsigaggen mataimakin gwamnan Zamfara 
Mahadi Aliyu Gusau.
PDP ta ce za ta ƙaddamar da kwamitin a ranar Alhamis a hidikwatar jam'iyya.