Zan Yi Wa Kowa Adalci A Gorancina---- Shugaban APC A Kano Tsagin Shekarau

Sabon shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Ahmadu Haruna Zago, wanda aka gudanar da zabensa jiya Asabar, daga tsagin tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa ba zai bari jam'iyyar APC ta karye ba, zai yi kokari wajen kaita ga nasara, musamman a babban zaben shekarar 2023 mai zuwa, kuma yace za iyi kokarin yin adalci ga kowa a cikin yan jam'iyyar. 

Zan Yi Wa Kowa Adalci A Gorancina---- Shugaban APC A Kano Tsagin Shekarau
Alamar APC

Sabon shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Alhaji Ahmadu Haruna Zago, wanda aka gudanar da zabensa jiya Asabar, daga tsagin tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa ba zai bari jam'iyyar APC ta karye ba, zai yi kokari wajen kaita ga nasara, musamman a babban zaben shekarar 2023 mai zuwa, kuma yace za iyi kokarin yin adalci ga kowa a cikin yan jam'iyyar. 

Taskira - H Online Tv ta rawaito cewa, Dan Zago ya bayyana haka ne jim kadan bayan samun nasarar da yayi a zaben, inda ya fara da godewa Allah, sannan yayi ga godiya ga Sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau, Sanatan Kano ta Arewa Barau Jibril Maliya, da sauran yan tawagarsu, cikin yaren Turanci.

A yanzu dai jam'iyyar APC a jihar Kano ta rabauta da samun shugabanni guda biyu, tsagin gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da suka gudanar da nasu zaben duk a jiyan, sun zabi Abdullahi Abbas domin ya cigaba da shugabantar jam'iyyar, wanda tuni ma ya saba layar rantsuwar kama aiki.

Yanzu abin jira a gani wanda uwar jam'iyar za ta goyi bayan shugabancinsa domin dukkan ɓangarorin suna iƙirarin jan ragamar.

Rikici ya kunno kai a jam'iyar tun lokacin da uwar gidan Gwamna Hafsat Ganduje wadda aka fi sani da Gwaggo ta bayyana wanda ake sa ran ya gaji Ganduje.