Ku Je Ku Yi Katin Zabe Domin Korar APC Daga Mulki-----Gimbiya Aisha Isa Katsina

Ku Je Ku Yi Katin Zabe Domin Korar APC Daga Mulki-----Gimbiya Aisha Isa Katsina

Daga Jamilu Dabawa, Katsina.

Tsohuwar yar takarar Sanatan Shiyyar Katsina Ta Tsakiya kuma daya daga cikin ta hannun damar dan takarar Shugaban Kasa, tsohan Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar ta yi kira ga al'ummar Najeriya da su fita su tabbatar da sun yi katin Zaɓe da ake cikin yi a halin yanzu, don ganin sun yi amfani da shi wajen korar Jam'iyyar APC da ta jefa yan Najeriya cikin mawuyacin halin yunwa da rashin tsaro da tsadar abinci da sauran matsaloli.

Hajia Aisha Isa Katsina ta bayyana haka a lokacin da take tattaunawa da manema Labarai kan kira ga mata da matasa da su je su yi katin kada Kuri'a a Katsina.

Gimbiya Aisha Isa Katsina ta kara da cewa Jam'iyyar APC ta jefa al'ummar Najeriya cikin halin kuncin rayuwa na fatara da yunwa ga matsalar rashin tsaro da maida mata da yawa jawarawa da maida yara da yawa marayu ga kuma uwa uba tsadar abinci. Ta hanyar amfani da wannan katin kadai ne za'a kakkabe wannan gwamnatin a shekarar 2023 daga sama har Kasa.