‘Yan Takarar Gwamnan Sakkwato A APC Nason Ayi Masu Zaben Kato Bayan Kato

‘Yan Takarar Gwamnan Sakkwato A APC Nason Ayi Masu Zaben Kato Bayan Kato

 

‘Yan Takarar Gwamna su 6 a Sakkwato sun rubutawa uwar jam’iyar APC ta kasa takardar suna bukatar a yi masu zaben kato bayan kato domin doka ta aminta da hakan.

‘Yan takarar da suka sanya hannu domin neman wannan bukatar ga uwar jam’iya su ne Sanata Abubakar Gada da Ambasada Faruk Malami Yabo da Sanata Ibrahim Abdullahi Gobir da Honarabul Yusuf Suleiman da Alhaji Abubakar Abdullahi Gumbi da Dakta Abdullahi Balarabe Salame.

A cikin ‘yan takarar su 7 dake son yi wa jam’iyar takara a zaben 2023,  Honarabul Ahmad Aliyu ne kadai bai tare da wannan ra’ayin na ‘yan takarar.

Duk kokarin jin dalilinsa na kin tafiya tare da takwarorinsa abin ya ci tura.

Honarabul Abdullahi Salame ya tabbatarwa Aminiya takardar dake yawo  daga wurinsu ta fito kuma duk wanda sunansa ya bayyana a takardar ya aminta da a nemi wannan bukatar ga uwar jam’iyar APC “Takardar gare mu ta fito domin muna son abaiwa kowa damarsa ta zama dan jam’iyya, duk abin da Allah ya yi za mu karbe shi.

“Mu duka ‘yan takarar shidda mun gamsu da a yi zaben kato bayan kato da fatar uwar jam’iya za ta duba kokenmu”, a cewar Salame.

A cikin takardar da suka rubuta ‘yan takarar sun nuna kan shari’ar da  ake yi a Sakkwato ta shugabanci yakamata a duba bukatarsu.

In ba a manta ba tun bayan kammala zaben shugabannin jam’iyar  ne a jihar bangaren Salame da Abubakar Gada suka kalubalanci gefen Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko a kotun Abuja, abin da aka yi ta tirka-tirka ba a kammala ba, kowane bangare na kiran kansa shi ne halastaccen shugaban jam’iya.

 Gobe Laraba ake sa ran kammala shari’ar a in da Alkalin Babbar kotun tarayya dake Sakkwato zai yanke hukunci dambarwa da ki ci ta ki cinyewa.