Rikici Ya Barke Tsakanin APC Da PDP A Sakkwato Kan Sarakuna Da Limaman Jumu'a

Rikici Ya Barke Tsakanin APC Da PDP A Sakkwato Kan Sarakuna Da Limaman Jumu'a

Musayar Kalamai a tsakanin PDP da APC a Sakkwato

Wani sabon rikici ya barke a tsakanin jam’iyar APC da PDP a jihar Sakkwato in da suke ta musayar kalamai kan danne hakkin mutane na bari su yi  jam’iyar da suke da shawa kanta da kuma magana kan sarakunan gargajiya a jiha.

Jam'iyar APC a wani bayani da ta fitar wanda shugabanta a jiha Isah Sadik Acida ya sanyawa hannu ya ce jam'iyar PDP a Sakkwato bayan ta samu koma baya kan rashin shugabanci mai inganci ta rude tana neman dubarun cilasta mutane su zabe ta da karfi, abin da ya kai ga sanya sarakunan gargajiya da limaman masallacin jumu'a shiga cikin yekuwar zaben PDP a jiha, wanda hakan kayar da martabar sarakuna ne da ita kanta dimukuradiyyar Sakkwato.

Ya ce yakamata gwamnatin jiha ta tuna sarakuna uwayen kowa ne dan siyasa da wanda baya siyasa a zahiri, kan haka yake kira da masu son daurewar dimukuradiyya su fita batun farfagandar PDP domin shiga jam'iyarsu.

Sadik Acida ya ce wata musgunawa da PDP ke yi wa mutane ita ce rike albashin kananan ma'aikatan kananan hukumomi da wasu jami'an ma'aikatar kananan hukumomi ke yi ba tare da laifin komai ba sai don su goyi bayansu, "yaushe ne bambancin ra'ayi ya zama laifi".

Shugaban ya nemi bayani ga hukumar kula da tsaftar birnin jiha a lokacin da aka cire masu allon tallata dan takararsu amma an bar na jam'iyar PDP a kafe.

"gwamnatin da ta kasa gyara titunan cikin gari da kauyukka bar maganar harkar noma, ita ce za ta biya SAs sabbi 2000 domin biyan bukatar siyasa".

A martanin da PDP ta mayar a wani bayani da sakataren yada labaran jam'iya Hassan Sahabi Sanyinlawal ya sanyawa hannu ya ce tun sanda Aminu Waziri Tambuwal ya zama gwamna bai taba yiwa wani Sarki a jiha barazaana ba abin da ke tsakaninsa da su girmamawa ne.

"Gwamnatin da ta gabata ne ta Aliyu Magatakarda Wamakko ba ta girmama sarakuna ba a yunkurinta na dole sai ta sanya wasu siyasa ta saukar da Uban kasar Dandinmahe da Yabo da Wamakko da Sabon Birni, kan haka yakamata APC su sani Tambuwal na girmama sarakuna fiye da magabacinsa Wamakko," a cewar Sanyinnawal.

Ya ce su a PDP suna biyar ka'idar da hukumar zabe ta gindaya ne, ba su yi wa ma'aikata barazana hakan ya sanya sakataren APC a jiha har yanzu ma'aikaci ne a jiha kuma ba a taba rike albashinsa ba.