Sambo, Fintiri Da Sauransu Sun Halarci Taron Tsayawar Atiku

Sambo, Fintiri Da Sauransu Sun Halarci Taron Tsayawar Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2023 a cikin jam’iyyar adawa ta PDP,  ya bayyana matakin da ya ɗauka a matsayin mai cike da tarihi tare da bayyana fatan 'yan Najeriya za su taka muhimmiyar rawa wajen ganin ya saamu nasara.

Atiku ya faɗi matsayarsa ne babban ɗakin taro na ƙasa da ƙasa dake Abuja a wurin an samu haƙartar tsohon mataimakin shugaban ƙasa Muhammad Namadi Sambo da Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri da tsohon Gwamnan Neja Babanhida Aliyu da Sanata Dino Melaye, da sauransu.

Kafin wannan rana ta aiyana takararsa Atiku ya karɓi fom na tsayawa takara da wasu 'yan kasuwa masoyansa suka saya masa, hakan ke nuna ya fito takara sai cigaba da neman goyon baya don samun tikitin takara a jam'iyar PDP.