A Karshe Dai Osinbajo Ya Aiyana Zai Yi Takarar Shugaban Kasa A 2023
Mataimakin shugaban kasar Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo a hukumance ya aiyyana kudirinsa na son ya shugabanci Nijeriya a 2023.
Ya bayyana matsayarsa ne a turakarsa ta Twitter a ranar Litinin da safe awoyi bayan ya sanar da kungiyar gwamnonin APC zai yi takarar shugaban kasa.
"A yau da dukkan mutuntawa, aa hukumance nake sanar da ku ina son zan yi takarar shugaban kasar Nijeriya a karkashin jam'iyar APC," haka ya fadi a faifan bidiyon da ya daura a Twitter.
managarciya