Ƙungiyoyin APC sun fara kira da a sauke  shugaban jam'iyyar na Kano 

Ƙungiyoyin APC sun fara kira da a sauke  shugaban jam'iyyar na Kano 

 

Kungiyoyin jam'iyyar APC da su ka haɗa da Ƙungiyar Ƙadangaren Bakintulu da ta Ƴan Takwas sun yi kira ga Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas da ya sauka daga kujerar shugabancin jam'iyyar saboda rigingimun da ya haifar a jam'iyyar.

Shugaban kungiyar Ƴan Takwas na jam'iyyar APC, Nura Na'annabi da sakataren kungiyar APC Kadangaren Bakintulu, Kwamared Abubakar Abdullahi Dangarinnan su ne suka bukaci hakan yayin wani taron manema labarai a yau Lahadi a Kano.

"A Madadin Kungiyar APC kadangaren Bakin Tulu ta Jihar Kano, mu na kuma yabawa  Dr. Abdullahi Umar Ganduje bisa Amsa kiraye- kirayenbmu da muka dade mu na yi na cewa ya sauka daga wannan kujera ta shugabancin Jam'iyar APC na Kasa, duba da irin rigingimu da zamansa a wannan kujerar ya haifar.

"Mu na yaba masa bisa irin kokarin da ya yi na ganin an samu shigowar wasu daga cikin Gwamnoni da Sanatoci da Ƴan Majalisar Tarayya da na Jihohi zuwa wannan Jam'iyar.

" Hakika abin a yaba masa ne kuma mu na masa fatan slheri a duk inda ya tsinci kansa nan gaba. "

"Mu na so kuma muyi amfani da wannan dama domin taya sabon Shugaban riko na Jam iyar APC His Excellency Bukar Dalori murnar kama aiki muna Addu'a Allah ya dafa masa. 

"Sannan muna so mu yi kira gare shi cewa ya yi gaggawar rushe shugabancin Jam'iyar matakin jihohi, musamman na nan Jihar Kano. Yin haka zai dawowa da Jam'iyar APC ta Jihar Kano kwarjinin da ta rasa tun bayan kasancewar Hon. Abdullahi Abbas a matsayin shugaban ta na Jihar Kano".

Com. Dangarinnan ya ce  "Idan kuma Allah yasa yaji kiraye kirayen da muke na cewa ya gaggauta sauka to Alhamdulillah. 

"Muna kuma kira ga shi sabon Shugaban Jam'iyar APC na kasa cewa lokaci ya yi da zai yi kokari wajen dinke kowace irin baraka da Shugabancin su Ganduje da Abdullahi Abbas su ka haifar mana na raba raben kawunan ƴan  Jmjam'iyyar, musamman a nan Jihar Kano,"