An yi nasarar daƙile ta'addanci a Katsina da kaso 70----Gwamnan Katsina

An yi nasarar daƙile ta'addanci a Katsina da kaso 70----Gwamnan Katsina

Kawo yanzu Mun cimma Nasarar Kawo Karshen ta'addanci a jihar Katsina da kaso saba'in 70 ~Gwamna Radda

Gwamna Dikko Radda na jihar Katsina ya ce gwamnatinsa ta rage yawan ‘yan fashi da makami zuwa kashi 70 cikin 100 a cikin shekara guda da ta wuce.

A cewar gwamnan, hakan ya biyo bayan yadda aka samu hadin kai tsakanin jami’an tsaron gida da na jami’an tsaro na yau da kullum a fadin jihar.