Shugaban ƙaramar hukumar Illela ta jihar Sakkwato Alhaji Sahabi Wakili ya sanar da cewa Ambaliyar ruwa ta tayar da gidaje sama da 300 a ƙaramar hukumar abin da ya sa dimbin mutane suka rasa mazauni.
Shugaban ya nemi taimakon gwamnatin jiha karkashin jagorancin Dakta Ahmad Aliyu Sokoto da ta taimaka wa mutanen karamar hukumar domin mutane suna cikin wahalar wurin zama in da suke labe a wuraren gwamnati kuma suma sun yi masu kadan.
Wakili a gaban Gwamna a lokacin da ya kai ziyara a ƙaramar hukumar ya ce "duk mutanen da ka gani sun zo tarbonka ban da wannan matsalar ruwa da sai sun fi haka yawa, mai girma gwamna a ƙaramar hukumar nan muna bukatar magudanun ruwa da samar da wani karamin gulb da ruwa za su taru a can.
"Koke ne da mutane ke son a duba masu, a gefen tsaro kashi 75 na karamar hukuma baya cikin rikon 'yan ta'adda hakan ya sa mutane da dama sun daina kwana garin Kwanni na ƙasar Nijar don ganin abubuwa sun samu sauki sosai," shugaban karamar hukuma kenan.
Gwamna Sakkwato a jawabinsa ya ce gwamnati ta kafa kwamitin da zai duba irin hasarar da Ambaliyar ruwa ta samar da kuma taimakon da za ta iya yi karkashin jagorancin shugaban Masu rinjaye na majalisar dokokin jiha Alhaji Bello Idris.
Gwamnan ya ce kwamitin ya zauna da shugaban riko na karamar hukumar, da zaran sun kammala aiki gwamnati za ta yi abin da take iyawa akai.
Gwamna Ahmad Aliyu ya ba sanarwar fara gyaran manyan masallatan jumu'a biyu dake kwaryar kamar hukumar da wasu hanyoyin mota.
Gwamnan bai tabo maganar gyaran hanyar da ta haɗa Illela da Gada ba duk da an yi korafi kanta, saboda aikin yafi muhimmaci sama da hanyoyin da gwamnatin jiha ta yi haɗin gwiwa da wasu hukumomi a duniya don aiwatar da su.