'Yan Sanda Sun Kama Kasurgumin Dan Bindigar Zamfara Da Ake Nema Ruwa Jallo 

'Yan Sanda Sun Kama Kasurgumin Dan Bindigar Zamfara Da Ake Nema Ruwa Jallo 

Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta ce jami’anta sun kama wani Isiyaku Babangida, kasurgumin dan bindiga da ake nema ruwa a jallo. Kakakin yan sandan jihar, Mohammed Shehu, ne ya sanar da ci gaban a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, jaridar The Cable ta rahoto. 

A cewar Shehu, an kama Babangida ne a yayin wani aiki da jami’an tsaro suka gudanar a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum da ke jihar.
“Jam’an yan sandan Zamfara, yayin da suke aikin fatrol, sun yi aiki kan wani bayanan sirri game da yunkurin da wasu guggun yan ta’adda karkashin shugabansu, Alhaji Bello ke yi na kai hari kan wasu garuruwa a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum. “Nan take jami’an yan sandan suka shiga aiki sannan suka fasa kai mabuyar yan bindiga da ke kusa wanda ya kai ga yin musayar wuta a tsakanin yan fashin da yan sandan. 
“Wutan da yan sandan suka bude ya sa sun yi nasarar daddake yan fashin, inda hakan ya tilasta masu tserewa da raunuka. “An kama wani dan fashi da ake neman ruwa a jallo mai suna Isiyaku Babangida na kauyen Kabe da ke jihar Kebbi.”