An Yi Jana'izar Mutumin da Aka Kashe Bisa Zargin Ya Yi Batanci a Jihar Sokoto 

An Yi Jana'izar Mutumin da Aka Kashe Bisa Zargin Ya Yi Batanci a Jihar Sokoto 

Hawaye sun kwaranya a wurin jana'izar marigayi Usman Buba, mahauci kuma mahaddacin Alƙur'ani wanda aka kashe bisa zargin ɓatanci ranar Lahadi a Sakkwato. 

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an ɓinne Usman bayan masa Sallar Janaza kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada a Masallacin Jumu'a da ke Mabera da karfe 2:30 na ranar Talata.
Dandazon jama'a ne suka tararwa Usman Buba da duka da sukar wuƙa har ya rasa rayuwarsa bayan wata gardamar aƙida ta shiga tsakani a babbar mahautar Sakkwato. 
Wannan kisan da aka yi wa bawan Allah ya bar baya da ƙura yayin da shaidun da aka yi komai a gabansu, suka ƙaryata zargin cewa ya yi wa Annabi SAW ɓatanci. 
Ɗaya daga cikin ganau, Nuhu Bala, ya ce ko kaɗan Usman bai yi kalaman ɓatanci ga fiyyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) ba kamar yadda makasan suka yi iƙirari. 
"Abinda ya faru Usman na yi wa wani Almajiri nasiha ne kan cewa ba'a amfani da sunan Manzon Allah wajen neman taimako. Nan wasu abokan sana'arsa da basu fahimce shi ba suka fara kiransa da kafiri." 
"Suka fara ihun ai ya ci mutuncin fiyayyen halitta ya yi kalaman ɓatanci ga Annabi SAW, suka fara jifansa da duwatsu, suna caka masa wuƙake."