'Yan bindiga Sun harbe mutum biyu tare da yi wa mata fyade a Sakkwato

'Yan bindiga Sun harbe mutum biyu tare da yi wa mata fyade a Sakkwato

'Yan bindiga sun harbi mutum biyu a kauyen Adamawa dake karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato.
Shugaban kungiyar 'yan sa-kai a yankin Musa Muhammad da aka fi sani da Bulaki  ya sanar da hakan ya ce harin ya faru ne a daren Lahadi, duk a cikin daren sai da suka sake mamaye  kauyen Rambadawa in da suka yi wa wasu magidanta duka da yin fyade ga wasu mata.
An samu labarin sun yi fashi da makami a Dantasakko da Nasarawa da Gidan Idi har sun tafi da baburan mutanen kauyen a gida biyu cikin gidajen da suka shiga.
A yankin akwai gungun mahara dake da shugabanni daban-daban wasu daga cikinsu akwai Nagona, Jambo Baki, Usaini Dan kwano, Dan Bakolo da Bello Turji da sauransu.
Akwai lokacin da aka samu labarin an kashe mutane 80 aka kori wasu daga gidajensu wanda Maharan suka yi.
Lamarin tayarda kayar baya a yankin 
ya yi sauki sosai abin da ya kawo mutanen karamar hukumar Isa ke bin hanyar Gundumi da gwamnati ta rufe tsawon lokaci kan matsalar tsaro, an bude hanyar duk da ba sanarwa a hukumance wurin gwamnatin jihar Sakkwato,mutane suna bi lafiya kalau daga Sakkwato har Isa.