Shirin Lahiya Sak Ya Tallafawa Mata 600 Da Murhun Gas a Sakkwato
*BAYARDA TALLAFIN MURAHUN DAHUWA NA ZAMANI (GAS COOKERS) GA MATA FIYE DA 600 KASHI NA DAYA (1) A SHIRIN: LAHIYA SAK MATAWALLE TAS MAI TAKEN: TUWON MALAM...MIYA TAI* *NAMA WANDA DANMAJALISAR WAKILAI BALARABE SHEHU KAKALE YA SHIRYA.*
Daga Mukhtar A Haliru Tambuwal Sokoto.
Kimanin Mata fiye da Dari Shidda (600) ne suka amfana da tallafin Danmajalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bodinga Dange-Shuni da Tureta Hon.Balarabe Shehu Kakale a ƙarƙashin wani shirin inganta rayuwar Mata kashi na Daya (1) wanda aka yiwa suna da Nana Asma'u yar Mujaddadi Shehu Usmanu Danfodiyo saboda irin gudunmawar ta akan inganta rayuwar Mata da sana'o'in dogaro da kai.
Wannan shiri mai taken: TUWON MALAM...MIYA TAI NAMA, MATA MU KORI HAYAKI nada manufar fadakarwa tareda tallafawa mata musamman mazauna yankunan karkara domin rage musu wahalhalun girke-girke duba da yanayin tsadar itace da kalanzir a matsayin makamashin girki.
A cikin wannan shirin, an raba Murahun Girke-Girke masu aiki da makamashin Gas (GAS-COOKERS) ga Matan dake a ƙananan hukumomin mulkin Bodinga, Dange Shuni da Tureta domin saukake musu wahalhalun girke-girke.
Ministan Lamurran Mata ta Najeriya, Dame Pauline Tallen ita ce ta kasance babbar bakuwa a yayin kaddamar da bayarda wannan tallafi ta hannun wakiliyarta Kuma Kwamishinan Ma'aikatar Lamurran Mata da Yara kanana ta jihar Sakkwato Hajiya Kulu Abdullahi Sifawa (Gimbiyar Sifawa). Muhimman mutanen da suka shedi wannan kasaitacen biki sun hada da, Kwamishinan Ma'aikatar Jin daɗin jama'a, jinkai da walwala Alhaji Abdullahi Abubakar Dange (Barden Dange), Shugaban kwamitin Yekuwar neman zabe na jam'iyyar PDP a ƙanan hukumomin mulkin Bodinga, Dange Shuni da Tureta Alhaji Abubakar Abdullahi Gumbi, Danmajalisar Wakilai Balarabe Shehu Kakale, Daractocin lafiya Alhaji Muhammad Sahabi Dange, Alhaji Abdullahi Sa'idu, Alhaji Aminu Liman, Uwar gidan ɗan takarar Gwamnan jihar Sakkwato a jami'ar PDP Hajiya Asiya Sa'idu Umar, Uwar gidan Danmajalisar Wakilai mai wakiltar Bodinga Dange Shuni da Tureta Hajiya Hauwa Abubakar Zaki, matan Kwamishinan Mai aikatar filaye da Gidaje, Hon.Aminu Bala Bodinga akwai Kwamishiniyar Ma'aikatar Ilimi mai zurfi Farfesa Aisha Madawaki Isah, mai baiwa Gwamna Shawara a fannin kungiyoyi masu zaman kansu da hakkin bil'adama Hajiya Ubaida Muhammad Bello, Sakatarorin dindindin Lubabatu Abubakar Kasim, Hajiya Aisha Turai Hassan, Shugabar Matan jam'iyar PDP ta jihar Sakkwato, Hajiya Kulu Abdullahi Rabah, Hajiya Hassana Dikko, Shugabannin Matan jam'iyar PDP a matakin kananan hukumomin mulkin Bodinga, Dange Shuni da Tureta da kuma Yankin Sakkwato ta Hajiya Aisha Muhammad Bodinga, Hajiya Rabi Muhammad Dange, Hajiya Sheri Abdullahi da Hajiya Halima Bawa Tureta.Akwai kansilolin Mata Hajiya Rabi Magaji, Hajiya Zainab Umar, Hajiya Rashida Umar, Murja Muhammad Dange, Inno Abubakar Kakale, da kungiyoyin sana'o'in dogaro da kai, Mambobin LAHIYA SAK, MTDi, MMAWT, MSO, SOZECOM, SAIEC, 21t CEHUB da sauran su. An dafa tuwaye da miyoyin Nama isashe a wurin taron harda kindirmon Nono domin karin lafiya ga alumma. Madogar labari...Hon. Musa Sabo. Mai magana da yawon Dan Majalisar tarayya Mai wakiltar Kananin Hukumomin Bodinga Dange Shuni da Tureta Hon Dr Balarabe Shehu Kakale
managarciya