Mu Lizamci Addu'ar Neman Zaman Lafiya Da Tsaro A Cikin Ramadan  ---- Ahmad Lawan 

Mu Lizamci Addu'ar Neman Zaman Lafiya Da Tsaro A Cikin Ramadan  ---- Ahmad Lawan 
Mu Lizamci Addu'ar Neman Zaman Lafiya Da Tsaro A Cikin Ramadan 
---- Ahmad Lawan 
Daga Awwal Umar Kontagora, a Abuja
Ina mai taya dukkan y'an Nijeriya, musamman al'ummar musulmi murnar zagayowar watan Ramadan mai alfarma. 
Watan Ramadan wata ne da musulmi a duk fadin duniya zasu gudanar da ɗaya daga cikin shika-shikan addinin musulunci, su taimaka ma abokan zaman su da kuma nuna ƙauna ga jama'ar da ke tare da su. 
Wannan lokaci ne na riƙo da addini, ƙauracewa, sadaukarwa da kuma gudanar da addu'oi ga Allah Subhanahu Wa Ta'ala. 
 Don haka watan Ramadan mai alfarma yana ba al'ummar musulmi dama ta kusantar ubangiji da kuma gudanar da rayuwar su ta hanyar da fiyayyen halitta, Annabi Muhammadu (SAW) ya koyar da mu. 
Manufar wannan lokaci na Ramadan yana da matukar tasiri a gare mu a halin da muke ciki na neman taimakon ubangiji domin fita daga Ƙalubalen da a yanzu suke damun Ƙasar mu. 
Gwamnatin Nijeriya tana yin duk abin da ya dace don samar da sauƙin al'amura tare da ammana da cewa akwai sauran aiki a gaba. 
Majalisar dokoki ta tarayya ba za ta sassauta ba a yunƙurin ta na tabbatar da ingantaccen shugabanci domin samar da tsaro, zaman lafiya da cigaban Nijeriya. 
Ga ƴan uwana musulmi, mu yi amfani da wannan dama ta watan Ramadan domin yin addu'oi ga ƙasar mu Nijeriya saboda imanin mu na Allah yana amsar addu'ar  bayin sa. 
Ina mai mana fatar yin azumin Ramadan cikin farin ciki da ƙoshin lafiya.