An kori wani ɗan siyasa a gidansa bayan matarsa ta jinginar da shi 

An kori wani ɗan siyasa a gidansa bayan matarsa ta jinginar da shi 

An kori tsohon dan takarar Gwamnan jihar Benue na jam'iyyar ACC, Ewaoche Benjamin Obe daga gidansa bayan matar sa ta bada jinginar gidan don karbo bashi.

DAILY POST ta rawaito cewa gidan yana unguwar Sagwari Layout a karamar hukumar Bwari ta birnin tarayya Abuja.

Matar mai suna Christiana Obe ta auri Obe ne tun shekarar 2006. Ma'auratan sun fito ne daga karamar hukumar Ogbadibo ta jihar Benue.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Laraba 25 ga watan Satumba na 2025.

Obe, wanda ke kan hanyar sa ta zuwa Benue ya samu kiran waya cewa wasu jami'an tsaron  sun dira a gidansa kuma sun fara shirin korar sa daga gidan.

Jin bacin rai kan lamarin, dan siyasar ya juya akalar motarsa zuwa gidan nasa.

Sai dai zuwan sa ke da wuya aka nuna masa takardun kotu dake nuni da cewa an karbe gidan nasa sakamon bashin da ake bin matar sa.

Sai dai yayin da ak la tuntubi matar tasa, sai ta kada baki ta ce "Ba dole ne sai na yi magana da kowa ba".