WATA UNGUWA: Fita Ta 15

Yanzu haka a can makarantar yake ci gaba da karantarwa. Ɓangaren iyalinsa kuwa alhamdulillah, ilimi na addini suna da shi dai-dai gwargwado, Bokon ma da ya tarar ana yi a birnin bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya saka yaransa. Yanzu haka Sadiƙu yana Jami'a, shekarunsa 28 a rayuwa. Sai Maheerah da take Ss3 shekarunta 18.

WATA UNGUWA: Fita Ta 15

BABI NA SHA BIYAR

 

 

Ganin Mahee bata da niyyar ko motsawa domin ta yi nisa sosai a cikin barcinta, hakan yasa bisa ga tilas Umman ta haƙura da tayar da itan ta koma ɗakinta ta zauna tana mamakin wannan barci haka. A ranta ta ce "Inta ta shi ai sai ta rama sallolin da bata yi ba, amma wannan barci..."

 

Maheerah kuwa bata farka ba sai wajajen 12:30 na dare. Da salati a bakinta ta buɗe idonta a hankali tana ƙarewa ɗakin kallo.

 

Jim ta yi na ɗan lokaci tana tuna abunda ya faru a yammacin ranar, da ƙarfi ta runtse idonta, wasu hawaye masu zafi suka sirnano mata.

"Astaqfurrullah! Astaqfurrullah!! Astaqfurrullahil azim!!" Abun da take ta maimaitawa kenan kafin ta buɗe idonta tana jin wani irin kunci da ya mamaye zuciyarta.

 

"Ka cutar da ni Ja'afar! Na ɗauke ka a matsayin masoyi nagari, ina yi maka kallon nagartaccen mutum ashe ban sani ba kura ce da fatar Akuya, ka zamo tamkar hankaka gabanka fari bayanka baƙi." Ta furta a hankali tana sauke ajiyar zuciya.

 

Wayarta ta janyo da nufin ta duba lokaci.

"Kai! Ashe haka lokaci ya ja ko sallar Magriba ban yi ba?" Ta furta da yanayin mamaki haɗe da takaicin halin da ta tsinci kanta a ciki.

 

Har zata ajiye wayar ta lura da misscalls ɗin dake gaban wayarta, cire key ɗin ƙaramar wayar ta yi tare da dubawa.

 

"Mtsww!" Ta ja wani dogon tsaki.

"Allah ya fika macuci kawai." Ta furta domin ganin kiran Ja'afar ne ta rasa.

 

Ajiye wayar ta yi sannan ta yunƙura daƙyar ta miƙe zuciyarta na mata zafi. Sai dai har zuwa lokacin jikinta baya da ƙwari ko kaɗan duk da cewa mayen ya sake ta.

A haka ta samu ta rama sallolinta sannan ta kuma kwanciya duk da idonta ya bushe ƙyam bako alamar barci.

 

Daren a haka ta kwana har gari ya waye bata rumtsa ba sai saƙe-saƙe  take a ranta.

 

Ta yankewa kanta hukuncin cewa ba zata sake ɗaga wayar Ja'afar ba, haka duk abinda zai sake kusanta ta da shi ba zata yi ba.

Ko da yake har yanzu ba wai zuciyarta ta haƙura da Ja'afar ɗin ba ne. Kawai tana so ne ya fuskanci girman kuskuren da ya aikata, sa'annan ita yar gidan Malamai masu daraja ce.

 

 

 

ASALINTA

 

MAHEERAH 'ya ce ga Malam Isah Saminu Kaita, Malam Isah haifaffen ƙauyen Kaita ne a cikin jihar Samburi dake ƙasar ta su.

Mahaifinsa ya kasance shararren Malami ne a ƙauyen nasu, su biyu ne kacal a gurin mahaifinsu daga shi sai ƙaninsa Sa'adu, sun ta so a ƙarƙashin kulawar malamin addini saboda haka suka kasance masu tarbiyya da ilimi sosai, da suka fara tasawa sai suka fara taya mahaifinsu aikin nasa na karantarwa a makarantarsa dake ƙofar gidan nasu. Kwanci tashi har su ma suka zama manyan Malamai da har suka so su zarta Mahaifin nasu.

 

Watarana kawai sai suka wayi gari da gawar Mahaifin nasu.  Mutuwar ta taɓa su sosai, bayan rasuwar mahaifin wani sirri ya bayyana a gare su cewa 'yan uwansa Malamai ne suka jefe shi saboda suna hassadar ɗaukakar da ya samu.

A lokacin sun ƙaryata wannan maganar a zahiri domin cewa suka yi "Ba wanda zai mutu sai in har kwanansa sun ƙare dama, kuma Allah ya faɗa a cikin alƙur'ani 'Kullu nafsin za'ikatul maut.'" don haka suka rufe wannan babin.

 

Sai dai wani abunda jama'ar garin da Malam Sa'adu ba su sani ba, wannan maganar ta tasirantu sosai a cikin zuciyar Malam Isah har ta ɗarsa masa tsoro. Dalilin kenan da ya sanya ya gayawa ɗan uwansa cewa shi zai matsa zuwa gari na gaba domin ya ci gaba da ba da karatu, sa'annan ya ƙaro ilimin zaman rayuwa domin shi ilimi kogi ne. Dama 'yan magana sunce zama guri ɗaya tsautsayi ne,  kuma ma ace kullum mutum yana zaune guri ɗaya tamkar kifin gwangwani?

 

Ba don Malam Sa'adu ya so ba a haka ya haƙura ya na ji ya na gani yayansa ya ɗauke matarsa da ɗansa suka bar gari.

 

Shi kanshi Malam Isah bai san inda ya nufa ba, kawai dai ya yanke idan ya je tasha duk sunan garin da ya fara ji can zai nufa.

 

Garin MAMBIYA ya fara cin karo da sunansa, hakan yasa ya nufi can kamar yanda suka yi alƙawari da zuciyarsa.

 

Bayan saukarsa garin sai ya nemi gidan haya a wata unguwa mai suna Bashal a nan ya fara zama shi da matarsa da ɗansa ɗan shekaru 8.

 

Ganin zama a haka baya yi ya saka ya fara taɓa kasuwanci da 'yan kuɗin da yayo guzurinsu daga ƙauyensu.

 

Bayan shekaru biyu ya koma ƙauye ya tattare sauran kadarorin da suka rage masa ya siyar ya haɗo kuɗin ya dawo MAMBIYA ya siyi gida a unguwar Garwa.

 

Lokacin Matarsa A'isha da yake kira Indo tana da ciki wata Takwas, suka tattare suka koma Unguwar ta Garwa.

 

Bayan wata ɗaya da tarewa Matarsa ta Haifi 'yarta mace santaleliya, duk da cewa duk kamannin Mahaifinsu suke ɗebowa amma jinjirar har ta so ta zarta shi a kyau.

 

Ranar suna yarinya ta ci sunan Maheerah 'yan'uwan Umma da Baba duk sun zo daga ƙauye. Bayan gama shagalin suna da kwana biyu suka koma gida.

 

A taƙaice dai haka Malam Isah da Indo suka ci gaba da renon yaransu (Sadiƙu da Maheerah) cikin kulawa da tarbiyya har zuwa lokacin da suka zama matasa.

 

Malam Isah da ya ga ba zai iya haƙura da harkar karantarwar ba duk da a yanzu tsoro take ba shi, sai ya je gurin wani Malami mai makarantar Allo a unguwar ya shaida mishi buƙatarsa.

 

Ba musu Malam Hadi ya Amince da wannan buƙatar, da yake duk harkar cuɗe ni in cuɗeka ce, washe garin ranar Malam Isah ya fita da dare lokacin da Malam Hadin ke yiwa magidanta karatu. A ranar tare suka bada karatun.

 

Malam Hadi ya sha mamakin ganin irin baiwar Malam Isah ta karatu da fasahar shi ta iya sarrafa harshe, har ya zarta shi a komai, dalili kenan da ya saka har ya ba shi shawarar ya kafa tashi makarantar.

Buɗar bakin Malam Isah sai cewa ya yi "A'a Malam Hadi ruwan da ya dake ka fa shi ne ruwa, ban ga dalilin da zai saka in kuma faɗawa tarko ina ji ina gani ba. Ka dai bari in taya ka kawai, duk ladar ɗaya ce ai."

 

Yanzu haka a can makarantar yake ci gaba da karantarwa. Ɓangaren iyalinsa kuwa alhamdulillah, ilimi na addini suna da shi dai-dai gwargwado, Bokon ma da ya tarar ana yi a birnin bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya saka yaransa. Yanzu haka Sadiƙu yana Jami'a, shekarunsa 28 a rayuwa. Sai Maheerah da take Ss3 shekarunta 18.

 

*Back to story*

 

Wasa-wasa sai da aka shafe kusan sati Ja'afar yana kiran Mahee a waya bata ɗauka, ga shi ya riga ya yiwa kansa alƙawarin ba zai koma gidansu ba, har zuwa lokacin da muradansa akanta za su cika.

 

Ganin bata ɗaga waya ya saka shi fara tunanin mafita, sosai yake mamakin yadda Mahee ta iya wannan ƙarfin halin don kuwa baya tunanin zata iya tumbuke dashen sonsa mai ƙarfi da ya yi a zuciyarta.

 

Wayar Duddoo ya karɓa ya kira ta da ita, da har ya fara tunanin ko dai ta samu wata matsala ne a gida, amma ga mamakinsa sai ta daga wayar.

"Assalamu alaikum." Ta yi sallama cikin muryarta mai daɗin sauraro.

"Wa'alaikumus salam" ya karɓa cikin muryarsa da yake ƙoƙarin sauyawa salo.

Bayan sun gaisa ta ce "Don Allah da wa nake magana?."

"Wani bawan Allah ne."

"Bawan Allah daga ina?" Ta kuma tambaya.

Murmushin takaici ya yi kana ya saki muryarshi ya ce "Hmm! Haƙiƙa na yi mamaki sosai yanda kika iya mantawa da muradin zuciyarki, har kin manta alƙawarin da muka yi na cewa ba rabuwa a tsakaninmu duk rintsi?"

Cikin marairacewa ya yi zancen.

 

Sai da ta ji wani sanyi ya saukar mata a zuciya da ta fahimci shi ne, amma ta dake ta fitittike ta gaggaya masa maganganu, domin tana tsananin buƙatar ya fahimci girman kuskurensa.

 

Ya ji matuƙar zafin maganganunta a ransa, amma ko alama bai nuna mata ba, haka ya yi ta lallaɓata domin ya samu ya mayar da ita ruwa.

 

Da ta fahimci cewa tausayinsa ya fara dirar mata kalamansa na neman yin tasiri a zuciyarta kawai ta katse wayar.

 

Sai dai kash! Aikin gama ya riga ya gama, domin kuwa bata ankara ba tuni yaudararrun kalamansa sun yi tasiri kuma sun samu muhalli a zuciyarta, ranar bata yi barcin kirki ba tunanin halin da yake ciki ne ya hanawa ƙwaƙwalwarta sukuni.

 

 

Washegarin ranar Mayenta ya zo gidansu tare da abokinsa Ma'eesh domin ya bata zance ko zata saurari Abokinsa.

*ZW*

 

amma a haka ta fatattake su da rashin kunyarta suka juya kowa ransa da ƙunci, a hanya suka haɗu da Yayanta Sadiƙu zai je gida.

 

Tsayawa ya yi ya miƙawa Irfan hannu ya ce "Assalamu alaikum, Mutumina an zo kenan?." Da murmushi a fuskarsa ya yi zancen.

 

Murmushin yaƙe ya yi bai ko tsaya amsa gaisuwar ba sai cewa ya yi "Eh yayanmu gani dai."

 

Ma'eesh kuwa sai aikin aikawa Sadiƙu da Harara yake, ganin Irfan yana ɓata masa lokaci da wata gaisuwar banza da ya tsaya yi, kawai sai ya yi gaba abinsa.

 

Bayan sun gaisa ne shi ma Irfan ya wuce yanayin fuskarsa ba walwala.

 

'Da wata a ƙasa, tabbas tana ƙasa tana dabo, kai Allah ya sa yarinyar nan ba halin banzan nata ta masu ba.' ya faɗa a ransa domin ya lura da yanda Abokin Irfan ɗin ke harararsa.

 

Dalilin kenan da ya saka ya yanke hukuncin ciwa Mahee mutunci idan har ya tabbatar da laifinta ne ya shafe shi.

 

Bayan kwana Uku ranar wata Talata Mahee ta yi shirinta tsaf na zuwa makarantar Boko.

Da misalin ƙarfe 7:30 ta fito cikin Uniform ɗinta sai ƙamshi take cikin hanzari ta fito daga ɗakinta ta nufi ɗakin Ummanta.

 

Da sallama ta shiga ɗakin inda ta tarar da iyayen nata suna karyawa.

 

Amsa sallamar Baba ya yi sannan ta durƙusa ta gaishe su, suka amsa.

 

Ƙara kallon fuskarta Umman ta yi sannan ta ce "A'ah! su Mahee yau har da kwalliya? Lallai yau kina ɗokin zuwa makarantar ko wani biki za'a yi a can ne?"

 

Murmushi ta yi ta ce "A'a Umma kawai dai na yi ne."

 

"Ba za a hukunta ki saboda haka ba?" Baba ya karɓe zance da jefa mata tambaya.

 

Faɗaɗa murmushinta ta yi ta ce "A'a Baba insha'allah ba abinda za a mun."

 

Umma ta ce "Shi ke nan ga naki Kunu da kosan zauna ki sha sai ki wuce."

 

Cikin ƙagara ta ce "Sauri nake Umma yau wani mugun Malami ne muke da first period bana so na makara."

 

"Shikenan a dawo lafiya." Umman ta faɗa.

 

Baba bai sake cewa komai ba Hannu kawai ya saka a aljihu ya ciro ₦200 ya bata.

Hannu na rawa ta karɓa da sauri ta yi waje ta saka sandals ɗinta ta fice cikin hanzari.

 

Wayarta dake maƙale a jakarta ta ji ta yi ƙara alamar shigowar saƙo, a soron gidan ta tsaya ta duba saƙon.

 

A bayyane ta ce "Uban azarɓaɓi kenan, ina hanya fa." Daga haka ta yi gaba abunta.

 

Isarta Titi ke da wuya ta samu Napep ta hau "Dagarma zamu." Ta faɗa tare da hawa bayan Napep ɗin.

 

Cike da mamaki mai Napep ɗin ya ɗan waiwayo kaɗan ya ƙara kallonta, a'iya saninsa ba wata makarantar 'yan mata a unguwar Dagarma Hasalima kayan jikinta sun nuna asalin makarantar da zata.

 

"Am! Baiwar Allah ko dai Unguwar Saminaka kike so ki ce? Na ga makarantar taku a can take." Ya tambaya a cikin mamakin da bai sake shi ba.

 

Cikin fishi da zafin rai Mahee ta ce "Ina sane, Bawan Allah idan ba zaka kai ni ba na sauka, gari da yawa....."

 

Gyara zamansa ya yi a mazauninsa ba tare da ya waigo ba ya ce "Allah ya baki haƙuri, zan je dama nema na fito."

 

Daga haka ba wanda ya kuma cewa Uffan a cikinsu har suka je Dagarman.

 

A ƙofar gidan da ta yi masa nuni ya faka. Nan fa ya ƙara cika da tsananin mamaki a ransa ya ce "Ikon Allah! Hali zanen dutse, sai ka ga mutum simi-simi kamar na Allah amma zuciyarsa cike take da datti. Ko da yake ƙaddara macece mara tabbas, haƙiƙa na tausayawa rayuwar wannan yarinyar da ta faɗa hannun 'yan bariki da ƙananun shekarunta....."

 

Yana tsaka da zancen zucin ya ji ta dungura masa kuɗi a gaban Napep ɗin a ɗan zafafe ta ce "Idan ka gama tunani sai ka ɗauki kuɗin ka tafi."

 

Yana nan gurin har ta shige gidan.

 

Kai tsaye ɗakinsu Ja'afar ta shiga, wannan karon ma cike take da fargaba sai dai ta yanke a ranta zata iya yin komai saboda farincikin masoyinta.

 

Yana ganinta ya wangale baki "Sannu da zuwa 'yar boko kuma 'yar Malamai."

 

Dariya suka hau yi su duka sa'annan ta zauna ba tare da ta ce komai ba.

"Babyna duk wanda ya ga shirin nan naki zai rantse da gaske makarantar za ki, to amma ya zaku kwashe da sauran yaran unguwa 'yan makarantarku da kuke dawowa tare?"

 

Sai da gabanta ya fadi da ta ji tambayar, domin ita kanta ta tabbatar akwai damuwa musamman idan aka yi rashin Sa'a yaya Sadiƙu ya biya ɗaukarta kaman yanda yake yi wasu lokutan, amma sai ta dake ta kawar da tsoro sa'annan ta yi dariya ta ce "Manta da su kawai, yanzu dai ga ni na zo ya aka yi?"

 

Daga inda yake zaune ya matso zuwa kusa da ita ya ce "Yawwa Babyna so nake ki zama wayayyiya kamar sauran mata, yanzu kai ya waye tuni an wuce waccan era kin ga dai ni ne zan aure ki sannan duk rintsi ba zan guje ki ba, ki yarda da ni."

 

Fara ja da baya ta yi, yanzu kam ta tabbatar da cewa Ja'afar ɗinta ya canza daga ainahin Jafseen da ta sani.

 

A haka sai da yasan yadda ya yi ya yaudare ta da yaudararrun kalamansa har ta kuma faɗawa tarkonsa a karo na biyu, sai dai wannan karon al'amarin ya fi ƙazanta domin ba a iya shaye-shayen kayan maye abun ya tsaya ba, sai da ya ja ta zuwa aikata ɓarna mafi muni.

 

Bayan awa huɗu Mahee ce ke tafe a galabaice fuskarta ta kumbura suntum, tafiya take kamar bata son taka ƙasa tsabar galabaita, abubuwane suka haɗu suka mata yawa, ga yunwar cikinta da ko ita kaɗai ta ishe ta, ga kuma zafi da raɗaɗin zuciya da gangar jiki da take ciki, a haka ta ƙaraso kan Babban titi ta tare Napep zuwa gida.

 

Ko a cikin Napep ɗin ba abunda take sai sauke ajiyar zuciya kallo ɗaya zaka mata ka tabbatar ta ci kuka har ta ba Uku lada.

Hannu ta saka a jaka daƙyar ta ciro wayarta, ba tare da tunanin komai ba ta goge lambar Ja'afar da duk wasu saƙwanninsa, duk wani abu da ya kasance zai tuna mata da Ja'afar a ranar sai da ta goge shi daga wayarta.

 

A take ta ji ta tsani kanta da take zaune da Ja'afar kuma ta kasa mantawa da shi, har zuwa wannan lokacin so da ƙaunar da take masa ba abunda ya ragu a ciki.

 

Dama ta goge duk wani abu da ya shafe shi ne a ƙoƙarinta na tursasawa zuciyarta tsanarsa da nisantar inda yake.

 

A haka har suka iso unguwarsu bata cikin nutsuwarta, ƙwaƙwalwarta duk ta hautsine.

 

Kai tsaye ta wuce zuwa gidansu tsabar damuwar da take ciki ta makantar da ita daga ganin magulmatan da ke zunɗenta a hanya.

 

Umma ta sha mamakin dawowar Mahee a dai-dai lokacin da take da yaƙinin ba a tashi daga makaranta ba.

 

Ko da ta tambaya ma bata samu wata gamsasshiyar amsar da zata yarda da ita ba, duk da ta tabbatar ba lafiya ɗin.

 

Ganin yanda Mahee ta shigo gidan tana tafiya a wawware kaɗai ya ishe ta shaidar ba lafiya kuma hakan ya ɗarsawa Umman fargaba.

 

"Shi ga ɗaki ki zauna ina zuwa." Umman ta faɗa ƙirjinta na lugude.

 

Bayan ta kaiwa Maheerah abinci ta ci ta bata magani, sa'annan ta shiga bincikarta da son sanin abinda ya faru.

 

Wani irin matsanancin kuka Mahee ta fashe da shi hakan ya ƙara jefa Umman cikin Fargaba da son sanin abinda ke faruwa.

 

A ranar ba a kwana ba sai da Umman ta fahimci ƙaddarar da ta faɗawa 'yarta.

 

Cikin matsananciyar damuwa ta shiga bawa 'yarta taimakon gaggawa tare da lallashinta da kwantar mata da hankali, domin wannan ba lokaci ba ne na tuhuma, ko zagi da duka. Lokaci ne da zata taimaki rayuwar yarta gurin ƙoƙarin ganin ta farfaɗo da martabarta da ta rasa.

 

Duk wata uwa mai hankali abunda ya kamata ta yi kenan, domin duka da zagi ba abunda suke haifar wa sai dai su saka yaro ya ƙara fanɗarewa.

 

Cikin dasasshiyar murya Umma ta ce "Shalelena ki yi haƙuri yau ɗaya ki zauna a ɗaki bana son ki fito waje ko kaɗan domin kada Malam ko yayanki su fuskanci halin da ake ciki."

 

Tana gama faɗa ta juya domin kuka na so ya ci ƙarfinta, ita kaɗai tasan halin da zuciyarta ke ciki game da wannan mummunar ƙaddarar da ta sami 'yarta a yau. Duk da tafi zargin fyaɗe aka yiwa yarinyar, tabbas kowaye ta bar shi da fitar rana da faɗuwarta, domin har gaban abada ba zata iya yafe masa ba.

 

A ranar haka Mahee ta wuni a ɗaki cikin tsananin nadamar rayuwa, a ranar sai da ta yi nadamar zuwanta duniya. Ta kuma tausayawa mahaifiyarta matuƙa da ganin irin halin da ta shiga ciki.

 

A ranar kaɗai ta ji ta yi nadamar sanin Ja'afar a rayuwarta, ta yi dana sanin wulaƙanta Irfan mai ƙaunarta da gaskiya. Shi ya sa aka ce abinda Babba ya hango yaro ko ya hau Rini ba zai hango ba.

 

A cikin waɗannan ranakun na ƙunci da kanta ta lalibo number Irfan da tunda take a rayuwa bata taɓa gwada kiransa ba, kuma ko ya kira bata ɗagawa.

 

Cikin zumuɗi Irfan ya kai hannu ya latsa screen ɗin wayar har hannunsa na rawa gun ɗaga kiran nata.

 

Ta shi ya yi zaune akan gadon don zuwa lokacin har ya shiga barci tunda dare ya riga ya yi ƙarfe 11:30.

 

Daƙyar kamar mai ciwon baki ta ce "Assalamu alaikum."

 

"Wa'alaikumus salam gimbiyata, dagaske ke kika kira ni ko mafarki na ke, irin wanda na saba?"

 

Cikin raunanniyar murya ta ce "Ni ce, don girman Allah ka yi haƙuri ka yafe mun, na sani bana kyauta maka." Sai ga hawaye shaa! Yana bin kuncinta.

 

"Oh! No baki mun komai ba, ki daina samun kanki a damuwa bana so." Ya faɗa cikin damuwa.

 

A haka ta yi ta ba shi haƙuri har zuwa lokacin da ta kashe wayar don kanta.

 

Ranar bai yi barci ba sai da ya kira Ma'eesh ya sanar masa, haka ya kwana cike da tsananin murna.

Barcinsa ma barci ne mai cike da mafarkan Mahee.

 

Bayan wasu yan kwanaki sati biyun da Abba ya ɗibarwa Mahee sun cika, don haka ya tuntuɓe ta da maganar.

 

Da kamar zata ce ta amince da auren Irfan sai dai tasan cutar da Irfan ɗin ne zata yi ba zata iya zama da shi ba.

 

Don haka ta kara bawa Baba haƙuri akan ya ƙara mata lokaci.

 

TUBAN MUZURU

 

Abunda Umma da Abba basu sani ba tuni Mahee ta sake jiki da Ja'afar ta kuma komawa gurinsa, yanzu da kanta take zuwa, duk lokacin da ta yi shirinta zata je makaranta ashe ba makarantar take zuwa ba, ɗakin Ja'afar take zuwa su aikata masha'arsu son ransu.

 

Duk ta gama sakankancewa da cewa shi zai aure ta abun auren ne kawai ba shi da a yanzu. Duk lokacin da ta yi masa maganar aure abunda yake faɗa mata kenan.

 

Watarana bayan fitar Mahee daga gida cikin shigarta ta makaranta, yaya Sadiƙu ya tare Napep suka bi bayanta.

 

Yana son sanin inda take zuwa idan ta fito da shirin makaranta domin tuni ya tabbatar ba makarantar take zuwa ba, domin ƙawarta Safina ta same shi ta gaya masa cewa Mahee tafi ƙarfin sati biyu rabonta da makaranta. Domin ya tabbatar da hakan watarana ya je makarantar tasu da misalin ƙarfe goma na safe, Malamai da wasu daga cikin Ɗalibai suka tabbatar masa da hakan. Shi ya sa a yau ya yanke hukuncin bin bayanta.

 

Ga mamakinsa sai ya ga Napep ɗin da take ciki ta nufi unguwar Dagarma. Ras kirjinsa ya buga da ƙarfi a ransa ya ce 'ya Allah! Allah ya saka abunda zuciyata ke raya mun ba haka ba ne, me Mahee take yi a wannan unguwar ta 'yan bariki?'

 

Kafin ya gama zancen zucinsa suka ƙarasa shigewa unguwar, wani layi can ƙasa ya ga sun nufa.

Can bayan wasu mintuna Napep ɗin ta tsaya ƙofar wani gida.

 

Leƙo kansa waje kaɗan ya yi yana leƙenta, "me nake shirin gani?" Ya furta da ɗan ƙarfi lokacin da ya ga Ja'afar ya fito yana dariya ya bawa Mahee hannu sun tafa, tana dariyar ita ma.

 

Wani irin raɗaɗi zuciyarsa ke masa kafin ya yi nasarar saukowa daga Napep ɗin tuni sun shige cikin gidan.

 

Da har zai je ya shiga gidan sai kuma ya fara tunanin ko dai zai jira ta ne ya ga minti nawa zata yi kafin ta fito? Yana so ya yi mata adalci ne shi ya sa ya gayyato kyakkyawan zato zuwa zuciyarsa, bai sani ba ko abu zata karɓa ta fito.

 

Can bayan mintuna 15 ya ga shiru kallon mai Napep ya yi "Bawan Allah don Allah jira ni kaɗan ina zuwa."

 

Lura da irin tashin hankalin da yake ciki ya saka mai Napep ɗin bai ce uffan ba ya tsaya jiransa.

 

Shi kuwa ya nufi ƙofar, tun kafin ya ƙarasa ciki ya ga samari da 'yan mata kala-kala suna shige da fice cikin gidan, duk da cewa lokacin safiya ce sosai.

Hakan ya sa bai yi wata-wata ba ya kutsa kai ciki,  shigarsa cikin gidan ya tabbatar da zarginsa na cewa gidan yan bariki ne.

Nan fa ya tsaya wuƙi-wuƙi yana nemanta ya ma rasa wane ɗaki suka shiga.

 

"Malam lafiya ka yiwa mutane tsaye ba magana?" Ya jiyo Muryar wani shaƙiyin a bayansa.

 

Ba tare da ya kalle shi ba ya ce "wata yarinya nake nema bata jima da shigowa nan ba, tana sanye da uniform a jikinta."

 

Gayen na jin haka ya tabbatar da budurwar Jafsee ake nema don haka ya kuma jefawa Sadiƙu tambaya cikin gadara.

"Meyasa zaka zo nemanta a lokacin da take cikin holewarta da gayenta, ba ma wannan ba meye matsayinta a gunka?"

 

Maganarsa ta farko ta mugun baƙantawa Sadiƙu rai amma akan tilas ya bashi amsa ko ya samu ya nuna masa ɗakin.

 

A ɗan zafafe ya ce "Ƙanwata ce nuna mun ɗakin da suka shiga."

 

Jin wannan furuci na matashin nan ya saka cikin fara'a gayen ya nuna masa daƙin, domin ya matsu ya ga ƙarshen Jafsee a gidan dama suna takun saka da shi, yasan yau ƙaryar Jafsee ta ƙare don da wuya  ya tsira.

 

Sadiƙu bai yi wata-wata ba ya banke Kofar ɗakin da suka kara ya faɗa ciki kai tsaye.

 

Tamkar mayunwacin zaki haka ya bayyana a gabansu lokacin sun riga sun sha kayen mayen nasu har suna tsaka da aikata masha'arsu.

 

Ƙafafun Sadiƙu suka hau rawa, ji ya yi kafufun nasa ba zasu iya ɗaukarsa ba, a binda ya ga ni a yau ko a mafarki baya fatar ganin makamancinsa akan kowacce ya balle tilon ƙanwarsa.

 

Jikinsa ya hau ɓari, a take ya ji wani ƙarfi ya zo masa, gani yake idan ya bar Ja'afar a haka tabbas ya gama cutarsu. Dalili kenan da ya saka ya yi kan Ja'afar ya cakumi wuyansa, sosai ya shaƙe shi yana kai masa naushi ta ko'ina.

Jafsee kam ba baki sai kunne ya kasa ƙwatan kansa, ko kaɗan jikinsa baida ƙwarin da zai iya wani motsi yana ji yana gani sai jibgarsa ake yana ihu.

 

Ita kuwa Mahee tsabar kunya da tsoro sun saka ta kasa miƙewa daga inda take jikinta sai kyarma yake kuka take sosai hawaye sai ambaliyya yake a idonta, a take sauran mayen da take ciki ya sake ta tsabar firgici, dama a ranar basu sha da yawa ba.

 

"Ke kuma Munafuka maciyiyar amana wacce bata kunyar ubangijinta ta shi maza ki shirya mu tafi." Ya daka mata tsawar da ta saka hantar cikinta ta kaɗa.

 

Iya firgici ta shige shi a ranar ba shiri ta miƙe ta hau kimtsa jikinta zuwa lokacin tuni 'yan kallo sun yiwa ƙofar dafifi.

 

Duddoo na ganin haka ya banke wasu gayu da suka zo ganin ƙwaf ya faɗa ɗakin tare da ƙoƙarin ceton abokinsa.

 

"Malam ka sake shi mana, ya zaka samu mutum har ɗakinsa kuma ka dinga dukansa?" Duddoo ya faɗa yana ƙoƙarin cire hannun Sadiƙu daga wuyan Jafsee.

 

Cikin huci da ɗaga murya Sadiƙu ya ce "Ba ruwanka Malam, da kai ka zo ka tarar da wannan ƙaton yana yaudarar ƙanwarka me kake tunanin zaka yi? Ya zaka ji.?

 

Duddoo har cikin ransa ya tausayawa wannan bawan Allahn yayan Mahee, hasalima ita kanta Maheen tausayinta yake, amma ba yanda ya iya dole ya kare Amininsa, hakan ya saka ya kawar da tunanin a ransa da cewa "Habah! Bawan Allah ka ga laifin ƙanwarka mana, ita ta kawo kanta fa, ko baka gani ba ne?"

 

Wannan zancen nasa ya saka ya saki wuyan Jafsee tare da faɗar "Gaskiyarka, ita ce mai asalin laifin don nan ba gidan ubanta ba ne, ita ta same shi." Ya na gama faɗa ya damki hannunta tare da kaura mata wani lafiyayyen mari da ɗayan hannun nasa.

 

Dama tuni ta gama shiryawa, tana kuka ya ja hannunta tare da ficewa daga gidan gaba ɗaya.

 

'Yan bariki kam sai kallo suke, masu yiwa Jafsee dariya na yi masu tausayinta na yi.

 

Mai Napep har ya fara gajiyawa da jiran Sadiƙu sai kuma ga shi ya gani ya na nufo shi riƙe da hannun yarinyar.

 

Suna zuwa bai ce komai ba ya jefa ta bayan Napep ɗin shi ma ya shiga..

 

"Bawan Allah mai da mu inda ka ɗauko ni." Ya faɗa cikin wata iriyar murya mai nuna tsantsan damuwa.

 

Har suka ƙarasa gida Mahee ta kasa ɗagowa ta kalle yaya Sadiƙu saboda tsananin kunyarsa da take ji a yau.

 

Ko da suka ƙarasa gida Baba yana nan bai fita ba. A tsakar gidan suka sami iyayen nasu, ingiza ta ya yi da ƙarfi ta faɗa a gaban Shimfiɗar Baba dake zaune.

 

"Meye ne haka Babba, ji mata ciwo kake so ka yi?" Umman ta jefa masa tambaya.

 

Baba bai ce komai ba sai binsu da ido yake.

 

Cikin muryar damuwa ya ce "Gata nan, na dawo muku da ita, daga yau ba zata sake yaudararmu da sunan karatu ba."

 

"Bangane ba Babba yi mana bayani." Cewar Umma tana kallon Sadiƙu dama haka take kiransa kasancewarsa ɗan fari, bata faɗar sunansa.

 

Ajiyar zuciya ya sauke kana ya masu bayanin komai tiryan-tiryan.

 

Salati suka saka a tare, Baba ya miƙe a zafafe, har lokacin Mahee na sunkuye a gabansa ta kasa miƙewa, tabbas a yau bata da bakin da zata iya yiwa iyayen nata magana haka ba wasu kalamai da zata iya kare kanta tunda an kamata dumu-dumu tana aikata zunubi mafi muni.

 

Wucewa Baba ya yi buzun-buzun ya ɗauko bulalarsa ta doki da yake amfani da ita a makaranta ya yo kan Mahee yana ta dukanta, tana ihu.

 

Sai da ya tabbatar ya farfasa mata jiki sannan ya haƙura, tsakanin Yaya Sadiƙu da Umma ba wanda ya yi yunƙurin dakatar da shi.

Zuwa lokacin wasu daga cikin maƙwafta na kusa da suka jiyo ihunta har sun zagayo don ganin meke faruwa.

 

Cikin tsananin ɓacin rai ya fara magana "Kin zubar mun da ƙima da darajar da nake da ita a idon duniya, ashe ban gaya miki ki nisanci wannan shaiɗanin saurayin naki ba amma kika ƙi? Ai ga irinta nan dama duk wanda ya ƙi ji ba ya ƙi gani ba, ga shi nan abunda ake guje mikin ya faru dake."

 

Ɗan dakatawa ya yi yana huci a hankali kafin ya ci gaba "Kamar yanda kika aikata abinda kike so ba tare da tunani ko yin shawara ba, ni ma haka zan yanke miki hukunci ba tare da sauraren shawara ko yin wani tunani ba, ba zan zauna da gurɓatacciyar halitta ba a gidana ba zan bari ki ƙazanta mun zuri'a ba....." Shiru ya yi kaɗan kafin ya dora

 

"Ki je na Kore ki daga gidannan, ko mai kama dake bana son ƙara gani, na fitar dake daga cikin zuri'ata ko bayan raina bana son wani ya alakantaki da jinina."

 

A tare Umma da yaya Sadiƙu suka zazzaro ido. Cikin ɓarin baki Umma ta ce "Haba Malam! Don Allah ka yi haƙuri ka da ka aikata abinda zaka zo ka yi nadama da ga baya."

 

"Kamar dai yanda na faɗa bana neman shawarar kowa, haka bana neman taimakon kowa, duk kuwa wanda ya yi ƙoƙarin taimaka mata ko da a cikin makwaftana ne ba zan taɓa yafe masa ba."

 

Sai a lokacin Mahee ta harhaɗo kalmomi daƙyar, tare da jan jiki ta matsa kusa da Baba ta dafe ƙafafunsa ta ce "Don girman Allah ka yi haƙuri Baba, na tuba, insha'allah ba zan sake ba kuma na maka alƙwarin zan auri Irfan."

 

"Allah ya kiyaye Irfan da auren irinki, da kika bata rayuwarki da ƙarancin shekarunki, ki je kawai." Ya faɗa.

 

Sai a lokacin Sadiƙu ya yi magana "Ina zata je Baba?"

"Ta je duk inda ta ga zata iya zuwa, yanzun ita kaɗai ce bata da dangi." Ya faɗa

 

Nan fa Umma da yayan suka shi ga ba shi haƙuri maƙwafta na taya su amma fir ya ƙi haƙura.

 

Ganin haka ya saka zuciyar Mahee ta ƙeƙashe a take ta ji tsanar Baban nata, don haka ta yunƙura daƙyar, ba tare da cewa kowa ƙala ba ta juya ta kama hanya da Uniform ɗin a jikinta.

 

Umman sai faman kiranta take tana kuka sosai "Mahee! Maheerah!! Don Allah ki tsaya. Malam ka dakatar da ita don Allah....."

 

Ita kam ko juyowa bata yi ba ta fice daga gidan cikin ƙuncin zuciya.

 

 

More comment more typing....

 

Tofah jama'a! Ina Mahee ta nufa.

 

Anyah wannan hukuncin da Baba ya yanke zai haifar masa da ɗa mai ido kuwa?

 

Ku biyo alƙalamin UMMU INTEESAR domin jin ci gaban wannan ƙayataccen labarin.