Tinubu Na Shirin Sanya Dokar Ta Baci a Kano Domin Kwace Mulki?

Tinubu Na Shirin Sanya Dokar Ta Baci a Kano Domin Kwace Mulki?

 
Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan zargin Sanata Rabiu Kwankwaso game da rigimar sarautar jihar Kano. 
Gwamnatin ta karyata zargin Kwankwaso kan cewa tana kokarin sanya dokar ta baci da kawar da gwamnatin Abba Kabir.
Kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya tabbatarwa The Nation cewa babu kamshin gaskiya a wannan zargi da aka yi. 
"Babu kamshin gaskiya kan wannan zargi na Kwankwaso, jita-jita ce kawai ake yadawa." 
"Babu yadda za a yi Gwamnatin Tarayya ta sanya dokar ta baci a jiha ba tare da hannun Majalisar Tarayya ba." 
"Majalisar Tarayya yanzu tana hutu babu shugaban kasar da zai tashi kawai ya sanya dokar ta baci a jiha." 
Wannan na zuwa ne bayan Sanata Rabiu Kwakwaso ya zargi Gwamnatin Bola Tinubu da neman dagula jihar Kano. Kwankwaso ya zargi gwamnatin ne game da halin da ake ciki yanzu inda ya ce suna jin shawarar makiyan Kano. 
Ya ce jami'an tsaron Gwamnatin Tarayya suna nuna goyon baya ga tubabben sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.
Sanatan ya bayyana haka ne yayin martani kan rigmar masarautun Kano a taron kaddamar da aikin hanya a Madobi.