Daga Babangida Bisallah, Minna
An bayyana cewar baccin da gwamnatin jihar Neja ta yi kan tantance yawan ma'aikata da 'yan fansho shi ke kawo tàna kashe kudade da yawa kuma jama'a su dawo suna kukan ba a biyan su hakkokan su.
Tsohon kwamishinan ilimi a jihar Neja kuma kodinetan cibiyar horar da harkokin siyasa, Honarabul Danladi Umar Abdulhamid Tambarin Kagara ya bayyana hakan lokacin da yake karin haske ga manema labarai kan nasarar da tantance 'yan fansho zai samar a jihar.
"A sanina bisa tsarin aikin gwamnati ya kamata kowane karshen shekara a tantance yawan ma'aikata da wadanda suka yi ritaya, wannan zai taimakawa gwamnati wajen sanin adadin kudin da ke tafiya wajen albashi da kuma abinda ke tafiya hannun 'yan fansho, haka kuma zai taimakawa gwamnati wajen sanin adadin ma'aikatan da suka mutu da kuma irin gurabun da suka kamata a cike.
"Amma bana tsammanin wannan gwamnatin tana yin wannan in ba yanzu da aka fara kan 'yan fansho ba, saboda haka ina yi mata fatan alheri akan wannan kyakkyawar niyyar da ta sanya a gaba, domin alamu sun nuna cewar aikin na tafiya yadda yakamata,"Kalamansa
Tambarin yayi kira ga ma'aikatan gwamnati da su ji tsoron Allah, domin halin matsin da 'yan fansho ke fuskanta 'yan uwansu ma'aikata ne suka jefa su ta hanyar kin yin abinda ya dace, da dan Adam mai tunani musamman ma'aikaci da ba su rika anfani da damar kujerarsu wajen tozartar da 'yan uwansu tsoffin ma'aikata ba, domin shi wannan dan fanshon ya samu kan sa a yau gobe kai ma za ka cinma wurin.
Hon. Abdulhamid, ya shawarci gwamnatin Neja da ta cigaba da bullo da hanyoyin da al'ummar jihar zasu mori mulkin dimukuradiyya a jihar, domin abinda ake nufi da dimokuradiyya shi ne samar da tubalin ginin kasa da cigaban al'umma, cigaban nan ba zai samu ba sai gwamnatin ta samu fahimta tsakanin da talakawan da suka zabe ta. Shi yasa tsarin shugabancin a siyasan ce, dan jama'a ne kuma na jama'a ne bisa fahimta da gamsuwa da muradun gwamnatin.