Gwamnatin Nijeriya Ta Gano Ma'aikatan Bugi dubu 50
GWAMANTAIN NIJERIYA TA GANO MA’AIKATAN BUGI DUBU HAMSIN
Sadiya Attahiru
Gwamnatin Nijeriya karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gano ma’aikatan bugi dubu hamsin(50,000) dake karbar albashi da sunan ma’aikatan kasa.
Dakta Mohammed K. Dikwa Sakataren kwamitin bincike na shugaban kasa(PICA) ne ya fadi haka a wurin taron karawa juna sani da ma’aikatar kudi ta kasa ta shiryawa manema labarai a satin da ya gabata. Ya ce a daftarin biyan kudin tsoffin ma’aikata 800 ke karbar albashi a ma’aikatu daban daban na gwamnatin tarayya da wasu ma’aikata dake aiki a halin yanzu 400 wasu ma sau biyu suke karbar albashi duk da na bugi ne kamar yadda aka gano, sai ma’aikata dubu talatin(30,000) da ba su cikin takardar karbar albashi amma ana fitar da kudinsu.
Ya kara da cewar a binciken da aka yi an samu nasarar tseratar da biliyan 208 dake zurarewa a cikin alljihun gwamnati da sunan biyan ma’aikata.
“Akwai ma’aikaci 681 dake amfani da asusun a jiya na albasi fiye daya”a cewarsa.
A tsarin kwarmato na busa usur kuwa Dikwa ya ce shirin ya samu nasarar gano biliyan 7.8, dala Amerika miliyan 378 da uro 27,800 a halin yanzu.
Haka kuma tiriliyan 8.9 kasar nan ta tara a tsarinta na tattara kudi a asusun bai daya(TSA), kamar yadda babban akawun gwamnatin tarayya Ahmad Idris ya baiyana a wurin taron karawa juna sanin.
Idris ya ce zuwa yanzu ma’aikatun gwamnati 1,674 ne ke cikin tsarin asusun bai dayan a kowane wata ana ajiye biliyan 40 a asusun.
Ya ce asusun(TSA) yana ]aya daga cikin tsarin da ya kar~u a }asar nan da ke taimakon gwamnatin tarayya ga rage dogaro da mai da tsakaita yawon kudi da samar da kudin shiga.
managarciya