Shugaban Majalisar Dattijai Ya Taya Tinubu Samun Nasarar Zaben Fitar Da Gwani

Shugaban Majalisar Dattijai Ya Taya Tinubu Samun Nasarar Zaben Fitar Da Gwani
Daga Awwal Umar Kontagora a Abuja.
Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan ya taya tsohon gwamnan Lagos kuma jagoran APC ta kasa, Bola Ahmad Tinubu murnar samun nasarar zaben fidda gwani na shugaban kasa da jam'iyyar ta gudañar a Abuja.
Ahmad wanda yayi takara da Tinubu ya bayyana zaben fidda gwani a matsayin wanda ya gudana bisa gaskiya, ya yi murnar samun nasarar tsohon gwamnan Lagos.
Yace sakamakon zaben ya nuna yadda tsohon gwamnan yake da kwarjini bisa amincewar yayan jam'iyyar, kamar yadda ya rubuta a sakon taya murnar ga manema labarai.
Ban tantama da rashin amincewar matsayin wakilan zaben na jam'iyya a kasar nan.
Bayan taya murnar samun nasarar da kuma amincewar sa ga yadda zaben ya gudana, Lawan ya bayyana cewar tsohon gwamnan Lagos din zai iya jagorantar jam'iyyar ga kai ga nasara a babban zabe mai zuwa a shekara mai kamawa.
Yace " Sakamakon kyakkyawàr ayyukan ka ga cigaban al'umma, kawar da kai dan cigaban jam'iyya da gudanar da shugabanci na gari zai baka damar samar da cigaban tsarin dimukuradiyya a kasar nan, ya sanya ma kwarin guiwar nagarta da amincewar yayan jam'iyya a kasar nan da yà kai ka ga samun wannan nasarar.
" A wannan rubutun, cikin koshin lafiya na ke taya murnar samun wannan nasarar dan ka cancanta.
“ Ba tantama akan cancantar ka, kwarewa, sanin makamar siyasa, jam'iyyar mu za ta samu nasarar babban zaben 2023, shugaban dattijan ya yi alkawarin zai cigaba da yin ayyuka da bada gudunmawa dan samun nasarar jam'iyyar.