Daga Abbakar Aleeyu Anache.
Dan majalisar wakilan tarayyar Najeriya mai wakiltar kananan hukumomin Zuru, Fakai, Danko Wasagu da Sakaba dake jihar Kebbi Honarabul Kabir Tukura, ya maganta akan matsalar tsaro da ya addabi al'ummar mazabunsa.
ont-size: large;">Tukura ya shaidawa majalisar wakilai cewa akalla kullum sai 'yan ta'adda sun kai farmaki a kauyukan Danko Wasagu da Sakaba, da yake wakilta yayin da yake bayanin halin da jihar su ta samu kanta sakamakon hare-haren 'yan bindigar.
Honarabul Kabir Ibrahim Tukura ya ce wa'dannan tarin 'yan bindigar dake dauke da muggan makamai na tafiya gari gari suna neman shanun da za su kwashe tare da kayan abinci da kuma satar mutane, in da suka mamaye wasu kauyuka irin su 'yan kade Mure 'yar kuka da wasu yankunan dake Sakaba da Danko Wasagu.
Tukura yace tabbas akwai rashin imani irin yadda bata gari ke bude wuta kan fararen hulla da jami'an tsaro musamman a arewacin Najeriya abu ne mai matukar tada hankali da kada zuciya.
Dan majalisar ya shaidawa majalisar wakilai da cewa yan ta'adda sun mamaye wasu yankunan Danko Wasagu, da Sakaba, lura da irin wannan kisa da kuma jikkata mutane da yan bindigar suka yi ta tabbata cewa cewar gwamnatin Najeriya da ta jaha basa daukar matakan da suka dace domin kare rayukan jama'a ganin yadda yan bindigar suka mamaye wasu yankuna suna iko da su wajen yin abinda suka ga dama.
Da yake tabbatar da adadin mai magana da yawun matasan yan majalisun Najeriya, yayi kakkausar suka dangane da hare-haren yan ta'adda.
A cikin wata sanarwa da ya fitar Tukura ya nemi gwamnatin Najeriya da ta dauke matakin gaggawa domin kawo karshen rashin tsaro da yan addabi yan kasa, ya kara da cewa muna jaddada kira ga jami''an tsaro da gwamnatin Najeriya da su kara zage dantse domin shawo kan wannan matsalar tsaro a arewacin Najeriya dama kasa baki daya.